A Kokarin Tserewa Sojoji Mai Garkuwa Da Mutane Ya Sheka Barzahu a Jihar Bauchi

A Kokarin Tserewa Sojoji Mai Garkuwa Da Mutane Ya Sheka Barzahu a Jihar Bauchi

  • Wani ɓata-gari ya sheƙa barzahu bayan ya yi ƙoƙarin tsere wa dakarun sojoji da ke a wajen shingen bincike a jihar Bauchi
  • Ɓata-garin dai ya yanke jiki ya faɗi ne inda ya ce ga garin ku nan bayan ya yi ƙoƙarin tsere wa dakarun sojojin
  • Dakarun sojojin sun kuma cafke wasu masu garkuwa da mutane da suka sace ɗalibar jami'ar tare da motarta inda suka ceto ta

Jihar Bauchi - Wani da ake kyautata zaton mai garkuwa da mutane ya gami da ajalinsa lokacin da yake ƙoƙarin tsere wa dakarun sojoji a jihar Bauchi.

Jaridar Aminiya ta kawo rahoto cew wanda ake zargin ya yanke jiki ya faɗi inda ya mutu nan ta ke a yunurin sa na tserewa sojojin.

Mai garkuwa da mutane ya mutu a Bauchi
Mai garkuwa da mutanen ya yi kokarin tsere wa dakarun sojoji Hoto: Thecable.com
Asali: UGC

Ɓata garin dai ya mutu ne bayan ya yi ƙoƙarin kauce wa wani shinen bincike na dakarun sojojin na ta 133 da ke a ƙaramar hukumar Azare cikin jihar Bauchi.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Hawaye Sun Kwaranya Yayin Da Jirgin Ruwa Dauke Da Mutane Da Dama Ya Kife a Jihar Kwara, Rayuka Da Dama Sun Salwanta

Sojoji sun cafke masu garkuwa da mutane

Haka kuma, sojojin sun yi caraf da wasu ɓata-gari mutum shiga waɗanda ake zargin masu aikata laifin garkuwa da mutane ne inda aka damƙa su a hannun jami'an ƴan sanda.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

SP Ahmed Wakili, kakakin rundunar ƴan sandan jihar, ya tabbatar da kama masu garkuwa da mutanen a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.

Kakakin ya bayyana cewa binciken farko-farko ya nuna cewa ɓata-garin sun yi awon gaba ne da wata ɗalibar jami'ar jihar Bauchi da ke a Gadau.

Ɓata-garin sun sace dalibar wacce ke zaune a unguwar Federal Low Cost cikin garin Azare, tare da motarta kirar Toyota Camry.

A cewar kakakin sojojin da ke aiki a shingen binciken sun tare waɗanda ake zargin bayan sun samu rahoto kan lamarin, inda suma ƙwace motar da ceto ɗalibar da aka sace ba tare da ta sami ko ƙwarzane a jikinta ba.

Kara karanta wannan

Gwamna Radda Ya Kwace Filayen da Gwamnatin Masari Ta Raba Wa Mutane a Katsina, Ya Faɗi Dalili

'Yan Daba Sun Sari Dalibi a Jihar Bauchi

A wani rahoton na daban kuma, wasu ƴan daba sun sari wani ɗalibin jami'ar Sa'adu Zungur da ke a Gadau, a jihar Bauchi da wuƙa.

Gardamar ƙwallo ce ta ɓarke a tsakaninsu wacce ta janyo aƙa aikata wannan mummunan ɗanyen aikin. An sari ɗalibin ne a wuyan hannunsa inda ya samu mummunan rauni.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng