NCC Ta Ba MTN, Airtel, Glo, 9mobile Wa'adin Daina Amfani Da Tsofaffin Lambobin Sa Kati, Data Da Sauransu

NCC Ta Ba MTN, Airtel, Glo, 9mobile Wa'adin Daina Amfani Da Tsofaffin Lambobin Sa Kati, Data Da Sauransu

  • Tuni kamfanonin sadarwar na ƙasa da suka haɗa da MTN, Airtel, Glo, da 9mobile suka fara amfani da sabbin lambobi na bai ɗaya wajen sanya kati, data, da sauransu
  • Hukumar sadarwa ta Najeriya (NCC), ta buƙaci duk 'yan ƙasa da ke amfani da wayoyin hannu da su san sabbin lambobin na bai ɗaya da aka zo da su
  • Hukumar ta kuma bayyana cewa daga ranar 17 ga watan Yunin 2023, duk tsofaffin gajerun lambobin da ake amfani da su a baya za su daina aiki.

Hukumar sadarwa ta Najeriya (NCC) ta yi bayani kan sabbin lambobin nan na bai ɗaya da aka umarci manyan kamfanonin sadarwa irin su MTN, Airtel, Glo, da 9mobile da fara amfani da su, sannan su daina amfani da tsofaffin.

A cewar hukumar, an tsara sabbin lambobin na bai ɗaya ne don taimakawa wajen sauƙaƙa ƙalubalen haddace lambobi daban-daban na sanya kati, duba kuɗi, siyan data da sauransu da masu amfani da wayoyi ke fuskanta.

Kara karanta wannan

An Yi Nasarar Dawo Da 'Yan Najeriya 109 Da Suka Maƙale a Libya Zuwa Gida

Hukumar ta NCC ta sanar da ranar 17 ga watan Yuni, 2023, a matsayin rana ta ƙarshe da za a dakatar da tsofaffin lambobin sannan a koma amfani da sababbin.

NCC ta ba MTN, Airtel, Glo da sauransu wa'adin daina amfani da tsoffin lambobi
NCC ta bai wa kamfanonin sadarwa na Najeriya wa'adin daina amfani da tsofaffin lambobi na kira, sa kati da sauransu. Hoto: Nigerian Communications Commission
Asali: Facebook

NCC ta bayyana sabbin lambobin na bai ɗaya

A cewar NCC, lambobin na bai ɗaya za su ba masu amfani da layuka daban-daban damar sarrafa layukansu cikin sauki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NCC ta ƙara da cewa babbar fa'idar lambobin ita ce bai wa masu amfani da layuka da yawa damar amfani da layukansu da lambobin kala ɗaya.

A cewar NCC:

“Sabbin lambobin na bai ɗaya za su yi amfani akan duka layukan kamfanonin sadarwar wayar hannu, wajen tuntubar ma'aikatan sadarwar, sanya kati, duba kuɗi, siyan data, da sauransu. Waɗannan gajerun lambobi duk iri ɗaya ne ga duka kamfanonin na sadarwa."

Yadda zaka tuna sabbin lambobin sa katin cikin sauƙi

Kara karanta wannan

Tsofaffin Gwamnonin Najeriya 5 Da Suka Fuskanci Ƙalubale Mako Guda Bayan Sun Bar Ofis

Hukumar ta NCC ta kuma bayyana yadda 'yan Najeriya za su iya tunawa da sabbin lambobin cikin sauƙi ba tare da wahalar haddace su duka ba.

Kamar yadda The Punch ta wallafa, NCC ta ce da zarar mutum ya danna *301# a wayarsa ta tafi da gidanka, zai ga jerin duka gajerun lambobin da yake buƙata sun bayyana.

Ana dai sa ran waɗannan sababbin lambobi na sanya kati, duba data, kiran kamfanin sadarwa da sauransu, za su sauƙaƙawa masu amfani da layukan sadarwa da dama wajen amfani da wayoyinsu.

Sabbin gajerun lambobin duka ɗaya ne ga masu amfani da MTN, Airtel, Glo, 9mobile da sauran duk wasu layukan kamfanonin sadarwa.

Ga wasu daga cikin sabbin gajerun lambobin na bai ɗaya na MTN, Airtel, Glo, 9mobile da kuma aikinsu a ƙasa:

  • Lambobin sanya kati — *311#
  • Lambobin duba ragowar kuɗin kira — *310#
  • Lambobin siyan data — *312#
  • Lambobin duba ragowar data — *323#
  • Lambobin rancen kuɗi — *303#
  • Hada lambar shaidar zama ɗan ƙasa (NIN ) — *996#
  • Duba tsare-tsaren da mutum yake a kai (VAS) — *305#
  • Lambobin tura kati — *321#

Kara karanta wannan

Tsadar Man Fetur: FRSC Ta Shawarci 'Yan Najeriya Su Koma Amfani Da Kekuna, Ta Fadi Dalilai

NCC ta gargaɗi 'yan Najeriya kan amfani da wasu wayoyi

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa a baya, hukumar sadarwa ta Najeriya (NCC) ta gargaɗi 'yan Najeriya kan amfani da jerin wasu wayoyi da hukumar ta ce na jabu ne.

NCC ta kuma sanar da cewa za ta ɗauki hukunci mai tsauri kan duk wanda aka kama yana siyar wa da mutane haramtattun wayoyin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel