An Yi Nasarar Dawo Da 'Yan Najeriya 109 Da Suka Maƙale a Libya Zuwa Gida

An Yi Nasarar Dawo Da 'Yan Najeriya 109 Da Suka Maƙale a Libya Zuwa Gida

  • Hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA), ta karɓi ‘yan Najeriya 109 da suka maƙale a birnin Tripoli na ƙasar Libya
  • Hukumar kula da ‘yan ci rani ta duniya (IOM) ce ta taimaka wajen dawo da waɗanda aka kwaso zuwa Najeriya
  • Rukunin waɗanda suka dawo sun haɗa da mata manya 46, yara biyu, jaririya guda ɗaya, maza manya 52, yara huɗu, da jarirai maza guda huɗu

Legas - Hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA), ta karɓi wasu ‘yan Najeriya 109 da aka dawo da su daga birnin Tripoli na ƙasar Libya.

Hukumar kula da 'yan ci rani ta duniya (IOM), ita ce ta taimaka wajen dawowa da mutanen zuwa filin tashi da saukar jiragen sama na Murtala Muhammad da ke Ikeja, birnin Legas.

An dawo da 'yan Najeriya daga Libya
An dawo da 'yan Najeriya 109 daga kasar Libya. Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Maza 60 da mata 49 ne aka dawo da su daga Libya

Kara karanta wannan

Wike: Tsohon Gwamnan Ribas Ya Bayyana Dalilin Da Ya Kamata APC Ta Yi Godiya Ga Allah, Ya Kuma Caccaki PDP

Daga cikin waɗanda aka dawo dasu akwai mata manya guda 46, sai yara biyu, da kuma jaririya guda ɗaya, kamar yadda Vanguard ta kawo a rahoto.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Baya ga haka kuma, akwai maza manya 52, yara huɗu da jarirai huɗu duk a cikin waɗanda aka dawo da su.

Daraktan hukumar bayar da agajin, Alhaji Mustapha Habib Ahmed, wanda ya samu wakilcin kodinetan ofishin hukumar na Legas, Ibrahim Farinloye ne ya tarbi mutanen.

Gwamnati za ta duba batun zuwa ci rani da matasa ke yi

Daraktan ya jaddada aniyar sabuwar gwamnati na tunkarar ƙalubalen da 'yan Najeriya da ke zuwa ci rani waje ke fuskanta.

Ya bayyana cewa sabon shugaban ƙasar ya bayar da tabbacin cewa gwamnatinsa ba za ta bar matasa a baya ba, saboda su ne ginshiƙan ci gaban duk wata al’umma a duniya.

Kara karanta wannan

Subhanallahi: Mutane Da Dama Sun Kone Kurmus a Wani Mummunan Hatsarin Mota a Jihar Kano

Ya kuma ƙara da cewa Shugaba Tinubu zai fito da wani tsari ga matasa maza da mata domin duba abubuwan da ya kamata a yi na ci gaba.

Ya ƙara da cewar za a bai wa matasa damar shigowa a dama da su a cikin al'amurran gudanar da gwamnatin ta Tinubu, duba da yawansu da kuma irin muhimmancinsu.

Daily Trust ta ruwaito cewa, daraktan ya ce gwamnati ta ba da tabbacin farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasa domin samar da ci gaba mara adadi.

Gwamnati ta kashe miliyan 560 wajen kwaso 'yan Najeriya daga Sudan

A wani labarin da muka wallafa a baya, kun ji cewa gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa ta kashe maƙudan kuɗaɗe har naira miliyan 560 wajen kwaso 'yan Najeriya daga ƙasar Sudan mai fama da rikici.

Ambasada Zubairu Dada, ƙaramin ministan harkokin ƙasashen waje ne ya shaidawa manema labarai hakan a Abuja.

Kara karanta wannan

Tsadar Man Fetur: FRSC Ta Shawarci 'Yan Najeriya Su Koma Amfani Da Kekuna, Ta Fadi Dalilai

Asali: Legit.ng

Online view pixel