Wanda Ake Zargi Ya Haura Ta Tagar Kotu, Ya Fece Bayan Alkali Ya Umurci A Kai Shi Gidan Yari

Wanda Ake Zargi Ya Haura Ta Tagar Kotu, Ya Fece Bayan Alkali Ya Umurci A Kai Shi Gidan Yari

  • Wani mutum mai suna Segun Akala, da ake tuhuma da laifin sata, ya tsallake tagar kotu kuma ya gudu bayan an ba da umarnin tsare shi a gidan yari
  • Sai dai ya yi rashin sa a, domin kuwa jami'an ‘yan sandan da ke harabar kotun, sun taimaka wajen cafko shi sannan kuma suka dawo da shi kotun
  • Amma kuma sa a ɗaya da ya yi ita ce, kotun ta amince da bayar da belinsa bisa tara ta kuɗi da kuma wasu sharuɗa da ta gindaya masa

Ondo - An ɗan samu wata 'yar ƙaramar dirama a kotun majistare da ke Odigbo, hedikwatar ƙaramar hukumar Odigbo ta jihar Ondo, yayin da wani da ake ƙara mai suna Segun Akala ya fece daga kotun bayan da alƙalin kotun ya bayar da umarnin tsare shi.

Kara karanta wannan

Majalisa Ta 10: Abdul'aziz Yari Ya Samu Gagarumar Nasara a Kotu Dab Da Zaben Shugaban Majalisa

The Punch ta tattaro cewa an kawo Akala gaban kotun ne bisa zargin sata, kuma an gurfanar da shi ne gabanta kan tuhumar hakan.

Wata majiya a kotun ta ce, alƙalin kotun, D. O Ogunfuyi, ya ba da umarnin tsare wanda ake ƙara, Segun Akala.

Mai laifi ya tsere daga kotu ana cikin shari'a a Ondo
Mai laifi ya fece ta tagar kotu ana tsaka da gudanar da shari'a a jihar Ondo. Hoto: The Cable
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wanda ake tuhuma ya tsere bayan jin hukuncin kotu a kansa

Da jin wannan umarni na kotun ne wanda ake ƙarar ya haura ta tagar kotun, sannan ya tsere zuwa cikin jeji duk da cewa akwai mari (handcuff) a hannunsa.

Majiyar ta ƙara da cewa sai da taimakon 'yan da ke harabar kotun aka yi nasarar cafko mai laifin.

Laifin da ake tuhumar wanda ake ƙara da shi

Ana zargin wanda ake tuhumar ne da satar sarkar injin yankan itace da kuma kayan sawa da kuɗinsu ya kai N336,000, mallakin wani mai suna Akintan Akintade.

Kara karanta wannan

Tsagerun 'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Basarake da Wasu Mutum 2 a Birnin Tarayya Abuja

Tun da farko, jami'in da ya shigar da ƙara, Usifo James, ya sanar da kotun cewa wanda ake ƙara ya aikata laifin ne a ranar 27 ga watan Mayun 2023 a titin Aipon, da ke Odigbo, jihar Ondo.

A cewar mai gabatar da ƙarar, laifin da aka aikata ya saɓawa sashe na 390 (9), na kundin laifuffuka na shekarar 200, na jihar ta Ondo.

Sai dai wanda ake tuhumar ya musanta laifin da ake tuhumarsa da shi.

Kotu ta bayar da belin wanda ake tuhuma

Lauyan mai gabatar da ƙara ya nemi a ɗage shari’ar domin ya samu damar yin nazari a kan fayil din ƙarar da kuma shirya shaidunsa, sai dai lauyan wanda ake ƙara, Mista Rufus Omotayo ya roƙi kotun da ta bayar da belin wanda ake karar.

Babban Alƙalin kotun, Ogunfuyi, a hukuncin da ya yanke, ya bayar da belin wanda ake ƙara a kan kuɗi N100,000 tare da sharaɗin kawo mutane biyu da za su tsaya masa, kamar yadda Naija News ta kawo.

Kara karanta wannan

Na Siyar da Jaririna Don Magance Matsalolin Iyali, Cewar Wata Mata a Yayin Da Ta Shiga Hannun Hukuma

Ya ba da umarnin a ci gaba da tsare wanda ake tuhuma a gidan yari na Okitipupa, har zuwa lokacin da sharaɗin belin nasa ya cika, sannan ya ɗage ci gaba da sauraron ƙarar zuwa ranar 23 ga watan Yuni, 2023.

Kotu ta yankewa basarake hukuncin ɗaurin shekaru 10

A wani labarin da ya faru kwanakin baya a jihar ta Ondo da Legit.ng ta kawo muku, kun ji yadda kotu ta yankewa wani babban basarake zama a gidan gyaran hali na tsawon shekaru 10.

An dai tuhumi basaraken ne da rusa ginin wata coci gami da lalata wasu bishiyoyi ba bisa ƙa'ida ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel