Cire Tallafin Mai: Yajin Aikin Da NLC Ke Shirin Zuwa Ya Gamu Da Cikas Yayin da Kawunan Kungiyar Ya Rabu

Cire Tallafin Mai: Yajin Aikin Da NLC Ke Shirin Zuwa Ya Gamu Da Cikas Yayin da Kawunan Kungiyar Ya Rabu

  • Zanga-zangar da NLC ke shirin yi kan cire tallafin man fetur da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi ya hadu da gagarumin cikas
  • An tattaro cewa kungiyar NLC reshen arewa da kudu maso yamma sun yanke shawarar janyewa daga yajin aikin da aka shirya farawa a ranar Laraba mai zuwa
  • Rabuwar kan kungiyar ya biyo bayan zargin da Bayo Onanuga, jigon APC ya yi cewa shugaban NLC, Joe Ajaero na yi jam'iyyar Labour Party aiki don tarwatsa kasar

Abuja - Kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta hadu da gagarumin cikas a shirinta na shiga yajin aiki a ranar Laraba, 7 ga watan Yuni.

A cewar jaridar This Day, alamu sun nuna cewa kawunan kungiyar sun rabu gabannin ranar da aka tsayar don fara yajin aiki yayin da kungiyar NLC reshen arewa da kudu maso yamma suka janye daga daukar wannan mataki.

Shugaban kasa Bola Tinubu
Cire Tallafin Mai: Yajin Aikin Da NLC Ke Shirin Zuwa Ya Gamu Da Cikas Yayin da Kawunan Kungiyar Ya Rabu Hoto: @officiaABAT
Asali: Twitter

Ci gaban na zuwa ne bayan Bayo Onanuga, daya daga cikin kakakin jam'iyyun All Progressives Congress (APC), ya zargi shugaban NLC na kasa, Joe Ajaero, da kokarin hargitsa kasar da sabuwar gwamnati yayin da yake yi wa jam'iyyar Labour Party aiki.

Dalilin da yasa yajin aikin da NLC ta shirya kan cire tallafin mai da Tinubu ya yi ba zai yi karfi ba

An tattaro a daren Asabar, 3 ga watan Yuni cewa an siyasantar da yajin aikin da NLC ke shirin zuwa kan cire tallafin man fetur da gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu ta yi, yayin da rassan kungiyar na kudu maso yamma da arewa maso yamma suka yanke shawarar janyewa daga zanga-zangar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sai dai kuma, domin ganin yajin aikin ya yi tasiri, shugaban NLC na kasa ya rubuta akalla kungiyoyi 43 wasika don su shiga yajin aikin da aka riga aka shirya yi, rahoton Punch.

Wasu daga cikin kungiyoyin da NLC ta rubutawa takarda sun hada da kungiyar malaman Najeriya (NUT), kungiyar malaman jami'a (ASUU), Kungiyar ma'aikatan shari'an Najeriya (JUSUN), kungiyar ASUN, Kungiyar NANNM da sauransu.

Wike ya goyi bayan Tinubu kan cire tallafin man fetur

A wani labarin, tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya goyi bayan cire tallafin man fetur da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi.

Wike ya ce dole sai an tauna tsakuwa idan har ana son a ciyar da kasar Najeriya gaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel