Jimami: Akalla Mutane 8 Sun Riga Mu Gidan Gaskiya, 6 Sun Samu Raunuka a Mummunan Hatsarin Mota

Jimami: Akalla Mutane 8 Sun Riga Mu Gidan Gaskiya, 6 Sun Samu Raunuka a Mummunan Hatsarin Mota

  • Hukumar FRSC reshen jihar Bauchi ta tabbatar da mutuwar mutane da dama a mummunar hatsarin da ya auku a hanyar Darazo
  • Hatsarin ya auku a ranar Laraba 31 ga watan Mayu, da misalin karfe 01:32 na rana yayin da jami’an hukumar suka isa wurin bayan mintuna 10
  • Mutanen da hatsarin ya afka da su, mutum 14 ne da suka hada da maza 5 da mata 6 sai kuma yara maza 2 da kuma yarinya mace daya

Jihar Bauchi Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) reshen jihar Bauchi ta tabbatar da mutuwar mutane takwas a wani mummunan hatsari da ya auku a jiyar Laraba 31 ga watan Mayu.

Hukumar a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba 31 ga watan Mayu, ta ce hatsarin ya faru ne da misalin karfe 01:32 yayin da jami’an hukumar suka isa wurin da misalin karfe 01:43 na rana.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kungiyar Kwadago Ta Dau Zafi, Ta Yi Watsi Da Sabon Farashin Man Fetur

Hukumar FRSC
Mutane 8 Sun Mutu, Yayin da 6 Suka Samu Raunuka a Mummunar Hatsarin Mota. Hoto: Daily Post.
Asali: Facebook

Hatsarin ya faru akan hanyar Darazo zuwa Bauchi wanda ke da cunkoso kullum kusa da kauyen Shadarki, cewar Tribune.

Daya daga cikin motocin da hatsarin ya afka da su akwai farar Toyota Hilux mai lamba BPP 041 da kuma farar VolksWagen Golf 3 da ake amfani da ita daukar fasinja.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yawan mutanen da hatsarin ya afka da su

Mutanen da hatsarin ya afka da su akalla sun kai 14 wanda suka hada da maza 5 da mata 6, sannan yara maza 2 da kuma yarinya mace daya, yayin da 6 daga ciki suka samu munanan raunuka.

Mutane takwas sun riga mu gidan gaskiya

Punch ta tattaro cewa akalla mutae takwas ne suka rasa rayukansu da suka hada da maza 2 da mata 3, sannan yara maza 2 da yarinya guda daya.

Kara karanta wannan

A banza: Peter Obi ya fadi abin da zai faru dashi bayan an rantsar da Tinubu

Mafi yawan raunukan da suka samu sun hada da kujewa da buguwar kai da kuma kaucewar kashi.

Hukumar ta yi gaggawan daukar wadanda abin ya rutsa dasu zuwa babban asibitin Darazo don basu kyakkyawan kulawa.

Mutane 8 Sun Riga Mu Gidan Gaskiya a Hatsarin Mota a Bauchi

A wani labarin, an rasa rayuka da dama yayin da mutane takwas suka mutu a wani mummunan hatsarin mota a jihar Bauchi

Hukumar FRSC ce ta tabbatar da haka inda ta ce hatsarin ya auku ne a kan hanyar Darazo zuwa Bauchi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel