Buhari Ya Rattaba Hannu a Kan Kudirin Dokar Almajiri da Hukumar Yara da Ba Sa Zuwa Makaranta

Buhari Ya Rattaba Hannu a Kan Kudirin Dokar Almajiri da Hukumar Yara da Ba Sa Zuwa Makaranta

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince a kafa hukumar kula da Almajirai a Najeriya a wannan karon
  • Wannan na zuwa ne bayan da wani kuduri ya tsallake cece-kuce da sukar ‘yan adawa a majalisar kasa
  • Ya zuwa yanzu, an ce za a samar da hukumar ne don daidaita zamantakewar ilimi da sana’a ga Almajirai

FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan kudirin dokar neman a kafa hukumar kula da Almajiri da yaran da ba sa zuwa makaranta domin hana gararanba da cin zarafin yara, Daily Trust ta ruwaito.

Kudirin ya samo asali ne daga abin da Balarabe Shehu Kakale da wasu mutane 18 suka gabatar kan batun da ya shafi waiwayar rayuwar Almajirai da yara masara zuwa makaranta.

Buhari ya kafa dokar kula da Almajirai a Najeriya
Shugaban kasa Muhammadu Buhari na Najeriya | Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Idan aka kafa ta, a cewar wadanda suka gabatar da kudirin, Hukumar za ta dauki nauyin samar da kwarewa ilimin rayuwa da kuma bunkasa shirye-shiryen kasuwanci ga yara da matasa, musamman Almajirai.

Kara karanta wannan

Bankwana: Buhari ya ba Sadiya Farouq lambar yabo saboda yadda take tausayin 'yan Najeriya

Buhari ya sanya hannu a kudurin

Da yake zantawa da wakilin Daily Trust a ranar Lahadi, dan majalisar tarayya Kakale (PDP, Sokoto), ya ce shugaban kasar ya sanya hannu kan kudirin ne a ranar Asabar yayin da ake bikin ranar yara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana kudurin dokar a matsayin wata katafariyar kyauta ga yaran Najeriya marasa galihu.

A cewarsa:

“Ina mika godiya ta musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa wannan gagarumar kyauta, mai girma, kuma raba gardama ga miliyoyin kyawawan kananan yara na Najeriya da sauran su.
"Ina taya daukacin masu ruwa da tsaki da 'yan kasa murnar wannan gagarumin aiki na tabbatar da adalci, daidaito da kuma hada kan ilimi a Najeriya inda ba za a sake barin wani yaro ko Almajiri a baya ba."

Wasu ‘yan adawa sun nuna rashin amincewa, amma kudurin ya tsallake

Kara karanta wannan

Mukamai 3 da Ake Sauraron Sabon Shugaban Kasa Ya Nada da Zarar Ya Shiga Ofis

Kudurin dai ya fuskanci adawa mai tsanani daga bangarori da kungiyoyi daban-daban na kasar nan tun bayan gabatar da shi.

Duk da haka, kudurin ya tsallake karatu uku, wanda hakan ke nufin abin da ya rage shi ne jin ra’ayin ‘yan kasa da sanya hannun shugaban kasa.

A halin da ake ciki, saura kasa da sa’o’i 24 a rantsar da sabon shugaban kasa a Najeriya, inda Buhari zai mika mulki ga Bola Ahmad Tinubu.

Tinubu zai yi nade-nade bayan karbar mulki

Ana kyautata zaton sabon shugaban zai yi nade-nade guda uku masu muhimmanci jim kadan bayan rantsar dashi.

Kakakin shugaban kasa, sakataren gidan gwamnati da shugaban ma'aikata na daga cikin wadanda Tinubun zai nada.

Asali: Legit.ng

Online view pixel