Yan Sanda Sun Cafke Fursunonin da Suka Tsere Daga Magarkamar Kuje Suna Aikata Wani Laifin a Adamawa

Yan Sanda Sun Cafke Fursunonin da Suka Tsere Daga Magarkamar Kuje Suna Aikata Wani Laifin a Adamawa

  • Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa sun yi nasarar cafke wasu fursunoni biyu bisa zargin satar shanu
  • Wadanda ake zargin sun tabbatar da cewa suna daga cikin wadanda suka tsere daga gidan gyaran hali na Kuje
  • Fursunoni da dama ne suka tsere a gidan gyaran hali na Kuje da ke birnin Abuja a watan Yuli na shekarar bara

Jihar Adamawa - Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta sake kama fursononi biyu da ake zargin sun tsere a gidan gyaran hali na Kuje a Abuja suna aikata wani laifin.

Fursunoni da dama sun tsere daga gidan gyaran hali na Kuje da ke birnin Abuja a watan Yuli na shekarar bara bayan ‘yan ta’adda sun yi amfani da abubuwan fashewa don fasa gidan gyaran halin.

Fursunoni a Najeriya
Fursunonin da Suka Fasa Magarkama a Kuje An Sake Kama Su a Adamawa. Hoto: Daily Post
Asali: Facebook

Premium Times ta tattaro ce wa akalla fursunoni 800 ne suka tsere daga gidan gyaran hali na Kuje a shekarar bara da ke dauke da fursunoni 994.

Kara karanta wannan

Mutane Hudu Sun Faɗa Komar ‘Yan Sanda a Ogun Bisa Laifin Halaka Makiyayi

Mafi yawa daga cikin wadanda suka tsere din an kama su a wurare daban-daban na fadin kasar, wanda yayin kai harin ya yi sanadiyar mutuwar jami’in tsaro da kuma fursunoni guda hudu, cewar The Guardian.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Rundunar 'yan sanda ta fitar da sanarwa

Kakakin rundunar ‘yan sandar jihar, Suleiman Nguroje a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin 22 ga watan Mayu, ya ce fursunonin biyu an kama su ne a kokarin da suke yi na satar shanu da sauran ayyuka munana.

Rundunar ta bayyana sunayensu da Atiku Ibrahim mai shekaru 37 da Adamu Ibrahim shi kuma mai shekaru 40 wadanda daman an dade ana nemansu ruwa a jallo tun bayan lokacin da aka fasa magarkama.

A cewar sanarwar:

“Lokacin da ake tuhumarsu sun tabbatar da cewa suna daga cikin fursunonin da ke Kuje tun shekarar 2021 bisa zargin safarar makamai, sun kuma tabbatar cewa sun gudo jihar Adamawa ne tun lokacin kafin a kama su yanzu.

Kara karanta wannan

Mazan Fama: Sojoji Sun Kai Samame Maɓoyar Yan Bindiga a Garuruwa 7, Sun Halaka Da Yawa

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Afolabi Babatola ya ba da umarnin a mika su ga jamia'an gyaran hali na jihar Adamawa don daukar mataki na gaba.

An Kama Fursunan da Ya Gudu daga Gidan Yarin Kuje a Nasarawa

A wani labarin, Yan sandan jihar Nasarawa sun cafke wani dan fursuna da ya gudu a gidan Yari na Kuje.

Wanda aka kaman, Salisu Buhari ya na daga cikin wadanda suka tsere da gidan gyaran hali na Kuje da ke birnin tarayya Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel