Shugaba Buhari Ya Naɗa Sabuwar Akanta Janar Ta Gwamnatin Tarayya

Shugaba Buhari Ya Naɗa Sabuwar Akanta Janar Ta Gwamnatin Tarayya

  • Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin sabuwar akanta janar ta tarayya tun bayan dakatar da tsohon akanta Ahmed Idris
  • Wannan naɗin na zuwa ne ƙasa da kwanaki goma da suka ragewa Buhari a matsayin shugaban ƙasar Najeriya
  • Shugaba Buhari ya amince da naɗin Dakta Oluwatoyin Sakirat Madein, wacce za ta fara aiki daga ranar Alhamis 18 ga watan Mayu

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya amince da naɗin Dakta Oluwatoyin Sakirat Madein, a matsayin babbar akanta-janar ta ƙasa.

Kamar yadda aka wallafa a shafin Tuwita na ma’aikatar yaɗa labarai da al’adu ta tarayya, nadin Dakta Madein ya biyo bayan zaɓen cike gurbi da aka gudanar.

madein
Shugaba Buhari Ya Naɗa Sabuwar Akanta Janar Ta Gwamnatin Tarayya. Hoto: @MBuhari, FMICNigeria
Source: Twitter

Za ta fara aiki daga 18 ga watan Mayu

An naɗa Dakta Madein ne a ranar Juma’a 19 ga watan Mayu a Abuja kuma naɗin na ta ya fara aiki daga ranar Alhamis 18 ga watan Mayun 2023.

Kara karanta wannan

Babban Jigo a PDP, Bode George, Ya Bayyana Dalilin Da Zai Hana Rantsar Da Tinubu a 29 Ga Mayu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An bayyana cewa shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya, Dakta Folasade Yemi-Esan, CFR ce ta sanar da naɗin na ta a Abuja, ranar Juma’a, 19 ga watan Mayu inda ta ƙara da cewa naɗin na ta zai fara aiki daga ranar Alhamis 18 ga watan Mayun 2023.

Dakta Madein dai za ta karɓi muƙamin daga hannun Mista Sylva Okolieboh, wanda shine akanta na riƙon ƙwarya tun bayan dakatar da Ahmed Idris daga muƙamin bisa zargin almundahana da almubazzaranci da dukiyar ƙasa.

Yanzu haka dai Ahmed Idris na fuskantar shari’a a gaban hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin kasa ta'annati (EFCC) bisa zargin almundahar wasu makudan kudade.

Ga sakon sanarwar kamar yadda aka wallafa a shafin ma'aikatar yada labaran:

Buhari ba shi da asusun banki da ya cika da kuɗin sata

A wani labarin da muka wallafa, mai taimakawa shugaban ƙasa kan harkokin watsa labarai Malam Garba Shehu, ya bayyana cewa shugaba Buhari ba shi da wani asusun banki da ya ke tara kuɗaɗen haram a ciki.

Ya bayyana hakan ne a wata hira da 'yan jarida, a lokacin da ya ke bayani kan yadda gwamnatin ta Buhari ke yaƙi da cin hanci da rashawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng