Babban Jigo a PDP, Bode George, Ya Bayyana Dalilin Da Zai Hana Rantsar Da Tinubu a 29 Ga Mayu

Babban Jigo a PDP, Bode George, Ya Bayyana Dalilin Da Zai Hana Rantsar Da Tinubu a 29 Ga Mayu

  • Jigon PDP, Cif Olabode George ya bayyana ra’ayinsa game da bikin rantsar da zaɓaɓɓen shugaban kasa, Bola Tinubu
  • Gabanin bikin na ranar 29 ga watan Mayu, George ya bayyana cewa idan har aka rantsar da Tinubu zai yi wuya a iya cire shi, ya kuma ce akwai batutuwan da ya kamata kotu ta warware
  • Jigon na PDP ya ƙara da cewa ba shi da wata matsala ta ƙashin kai tsakaninsa da Tinubu, amma lallai bai ci Abuja ba, saboda haka bai kamata a yi bikin rantsar da shi ba

Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Cif Olabode George, ya bayyana ainihin dalilin da ya sa babu tabbacin a rantsar da Tinubu a ranar Litinin, 29 ga watan Mayu.

A wata hira da ya yi da jaridar Guardian, Bode George ya yi bayanai ƙwarara kan dalilin da yasa za'a dakatar da rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Muhimman Abu 2 da Suka Jawo Allah Ya Hana Atiku da Peter Obi Mulkin Najeriya a 2023

Tinubu and George
Bode George, Ya Bayyana Dalilin Da Zai Hana Rantsar Da Tinubu a 29 Ga Mayu. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Bode George
Asali: Facebook

Me ya sa ba za a rantsar da Tinubu ba, Bode George ya ba da dalili

George ya bayyana cewa akwai manyan batutuwa masu muhimmanci a gaban kotu da ya kamata ace ta warware kafin a rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bola Tinubu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da yake ƙarin haske, Geroge ya kuma ce, zaɓaɓɓen shugaban ƙasar bai cika dukkan ƙa'idojin da ake buƙata don lashe zaɓen ba, don haka bai ma kamata a yi bikin rantsar da shi ba.

A kalamansa:

“Shin Tinubu ya samu kaso 25% cikin 100% a Abuja? waɗannan wasu batutuwa ne masu muhimmanci da muke neman kotun koli ta warware mana su tukun, shi (Tinubu) bai ci Abuja ba, bai kamata a yi bikin rantsar da shi ba.”
“Kundin tsarin mulkin kasar nan bai tsara cewa dole sai a ranar 29 ga watan Mayu ne za a yi rantsuwar ba, idan akwai muhimman batutuwa, to a gama warware su, ba maganar a yi wata gwamnatin rikon kwarya ba, shugaba Buhari ba zai sauka ba, sai ya ci gaba da riƙe ƙasar har sai an ƙarƙare batutuwan da ke gaban kotu."

Kara karanta wannan

Jerin Sunayen Manyan ‘Yan Siyasar da Ake Tunanin Tinubu Zai Naɗa Ministoci In Aka Rantsar Da Shi

Bai kamata a rantsar da Tinubu ba har sai kotu ta yanke hukunci, inji Bode Gorge

Da yake amsa tambayoyi kan kasancewarsa mai kakkausar suka ga zaɓaɓɓen shugaban ƙasa da kuma dalilin da ya sa yake ganin ba za a rantsar da shi ba, Bode George ya ce bai kamata a rantsar da Tinubu a ranar Litinin, 29 ga watan Mayu ba har sai kotu ta gama yanke hukunci.

Ya kuma ƙara da cewa, Tinubu ya yi masa laifuka da dama. Sannan kuma ya bayyana cewa duk hukumar zaɓe ta ƙasa INEC ce ta jawo wannan hayaniyar da ake ciki a yanzu.

Daga ƙarshe, George ya ce har yanzu zaɓe fa bai ƙare ba tunda dai akwai ƙorafe-ƙorafe a gaban kotun ƙarar zaɓe.

A saboda haka ya ce babu batun ma a riƙa maganar wanda ya lashe zaɓe ballantana kuma maganar bikin rantsar da shi.

Peter Obi ya yi zazzafan martani kan wayar sakataren Amurka da Tinubu

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi: Babu Wanda Zai Iya Hana Rantsar Da Tinubu

A wani labarin namu na baya, ɗan takarar shugabancin ƙasa ƙarƙashin jam'iyar Labour Party, Peter Obi, ya yi martani mai zafi kan kiran wayar da sakataren harkokin wajen Amurka, Anthony Blinken ya yi da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bola Tinubu.

Har yanzu dai ba a iya samun cikakkun bayanai kan abinda Tinubun ya tattauna da Blinken ɗin a wayar ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel