Bautar Ƙasa: Bai Kamata Shirin NYSC Ya Zama Wajibi Ba, Farfesa Jega

Bautar Ƙasa: Bai Kamata Shirin NYSC Ya Zama Wajibi Ba, Farfesa Jega

  • Farfesa Jega ya bayyana cewa bai kamata shirin yi wa ƙasa hidima wato NYSC ya zama wajibi ga ɗaliban Najeriya ba
  • Ya ce kamata ya yi shirin ya zama na waɗanda suke da ra'ayin yi ne sannan kuma suka kammala karatu da sakamako mai kyau
  • Mataimakin gwamnan jihar Oyo, Adebayo Lawal, ya nuna goyon bayansa ga yadda ake gudanar da shirin yi wa ƙasar hidima a yanzu

Abuja - Farfesa Attahiru Jega, tsohon shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), ya bayyana cewa bai kamata tsarin yi wa ƙasa hidima (NYSC) na shekara ɗaya ya zama wajibi ba.

Da ya ke jawabi a wajen bikin cikar NYSC shekaru 50 da aka yi a Abuja ranar Litinin, ya ce idan har akwai wani aiki da zai zama na dole, to sai dai aikin soja kawai.

Kara karanta wannan

Ikon Allah: Yan Uwan Juna Sun Baiwa Hammata Iska Kan Kuɗin Sadaƙin Yar Uwarsu N250,000

Ya ce bai kamata shirin ya zama dole ko da ga ɗalibai masu hazaƙa da suka samu sakamako mai kyauwu ba kamar yadda Daily Trust ta yi rahoto.

Masu yi wa ƙasa hidima
Matasa masu yi wa ƙasa hidima na shirin NYSC. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Waɗanda ke ra'ayi kaɗai ya kamata a zaɓa - Attahiru Jega

A cewarsa, ɗaliban da suka nuna ra'ayinsu ya kamata a zaɓi mafiya hazaƙa daga cikinsu, sannan a tanadar musu wadatattun kuɗaɗe da za su basu damar yin aiki cikin nutsuwa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jega ya kuma ƙara da cewa a bai wa waɗanda aka zaɓa horo ta yadda za su iya riƙe manyan muƙamai a ƙasar bayan sun kammala.

Sai dai ya jaddada cewa idan har shirin zai zama tilas ga ɗumbin ɗaliban da ake yayewa daga manyan makarantun ƙasar nan, to dole ne a samar da duk abubuwan da za su buƙata a yayin hidimar.

Kara karanta wannan

Majalisa Ta 10: Dalili 1 Rak da Yasa Tinubu da APC Suka Zabi Akpabio da Abbas, Shettima Ya Tona Gaskiya

Alawus ɗi masu bautar ƙasa ya yi kaɗan, In Ji Jega

Jega ya kuma ƙara da cewa, albashin da ake bai wa masu bautar ƙasar ya yi kaɗan, wanda na faruwa ne sanadiyyar mutanen da ake ɗauka da yawa.

Sannan kuma ya shawarci a kula da yanayin tsaron masu bautar ƙasar domin a kawo ƙarshen kiran da wasu ke yi na cewar a dakatar da shirin baki ɗaya.

Daga cikin irin ƙalubalen da ya ce shirin na fuskanta akwai rashin samun goyon bayan wasu gwamnatocin jihohi da na ƙananan hukumomi wurin ciyar da shirin gaba.

Hakanan Jega ya kuma bayyana cewa wasu makarantun kan shigar da ɗaliban da ba su cancanta ba cikin shirin, wanda wannan ma wani ƙalubalen ne.

A cewarsa:

“Ina mai ba da shawarar a sanya NYSC ya zama abu ne na ganin dama. A zaɓi ɗalibai masu hazaƙa da ke da sha'awar shiga shirin, sannan kuma a samar musu da isassun kuɗaɗe, kayan aiki, horarwa ta yadda za su iya riƙe manyan muƙamai na musamman a kasar nan.”

Kara karanta wannan

"Mahmud Yakubu Tsohon Yaro Na Ne," Pater Obi Ya Fallasa Maganar da Ya Faɗa Wa Shugaban INEC Gabanin Zaben 2023

"Duk wani shiri da ba shi da alaƙa da aikin soji, to bai kamata ya zama wajibi ba, musamman idan abu ne da ake so a cimma wata manufa ta musamman da shi."

Sai dai The Guardian ta ruwaito Jega ya na faɗin cewa, duba da irin rawar da shirin ya taka a baya, akwai yiwuwar ya taimaka wajen ci-gaban ƙasar a nan gaba.

Mataimakin gwamna ya goyi bayan wajibantar da NYSC

Sai dai kuma shi a nashi ra'ayin, mataimakin gwamnan jihar Oyo, Adebayo Lawal ya goyi bayan cewa shirin hidimar shekara dayan ya zama wajibi.

Ya ce samuwar shirin ya taimaka wajen ƙara samun tarbiyya ga matasan da suka bi ta cikinsa, sannan kuma shirin ya taimaka wajen samun ƙaruwar haɗin kai da ci-gaban ƙasa.

Ya ƙara da cewa shirin ya taimaka wajen tabbatar da ingancin digirin da wasu manyan ƙasar nan da dama suka ce sun samu.

Kara karanta wannan

Fitaccen Gwamnan APC Ya Naɗa Sarakunan Gargajiya Sati 2 Kafin Ya Bar Ofis

Ya ce hukumar NYSC ce ke tabbatar da sahihancin karatun da yawancin ‘yan siyasar ƙasar nan ke iƙirarin sun yi.

Wata gajeruwar mata ta haɗu da mijin da za ta aura a sansanin 'yan bautar ƙasa

A baya mun kawo muku labarin wata mata mai ƙanƙanin jiki da ta samu saurayin da za ta aura a sansanin horas da masu yi wa ƙasa hidima.

Labarin matar mai suna Innocent Ruth ya yi fice sosai a kafafen sada zumunta, inda ta bayyana cewa saurayin da za ta aura ya fi kowa tsayi a sansanin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel