Mahmud Yakubu Ya Yi Aiki Karkashina Kafin Zama Shugaban INEC,Peter Obi

Mahmud Yakubu Ya Yi Aiki Karkashina Kafin Zama Shugaban INEC,Peter Obi

  • Ɗan takarar shugaban ƙasa a zaben 2023, Peter Obi, ya bayyana cewa ya fi kaunar ganin an yi gaskiya maimakon kamun ƙafa
  • Ya ce bai damu da duk tsawon lokacin da za'a ɗauka gabanin gaskiya ta yi halinta ba, amma tilas doka ta yi aikinta
  • Yayin da yake jawabi a Awka, Obi ya ce shugaban INEC na yanzu yaronsa ne a baya amma bai taɓa neman kamun ƙafa da shi ba

Awka, Anambra - Ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar LP, Peter Obi, ya bayyana dangantakarsa da shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Mahmud Yakubu.

A wurin kaddamar da littafinsa ranar Jumu'a 12 ga watan Mayu, 2023 a Awka, babban birnin jihar Anambra, Obi ya ce Yakubu ya taɓa aiki a karƙashinsa wani lokaci a baya.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: "Ba Makawa Dole Na Zama Shugaban Kasa a Najeriya," Peter Obi

Kamar yadda Daily Trust ra rahoto, Obi ya ce duk da haka bai taɓa yunkurin tunkarar Yakubu ko ya nemi ya masa alfarma ba gabanin zaben shugaban ƙasa.

Obi da Yakubu.
Mahmud Yakubu Ya Yi Aiki Karkashina Kafin Zama Shugaban INEC,Peter Obi Hoto: Mr Peter Obi, Olukayode Jaiyeola
Asali: Twitter

A kalamansa, Obi ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"A baya na rike muƙamin shugaban kwamitin TEFFUND, kuma Farfesa Mahmud Yakubu mambana ne a lokacin. Mun san juna amma tunda ya zama shugaban INEC, ban taɓa zuwa wurinsa ba."
"Na faɗa masa yanzu kai ne Alkali, ka tabbata kayi abinda da ya dace. Idan ka samu damar yin abinda ya dace amma ka zabi kawo hargitsi, to kowa zata shafa. Ina nan kan baka ta dole sai an yi gaskiya."

A halin yanzun, tsohon gwamnan Anambra ya fara fafatawa da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, a kotun sauraron ƙararrakin zaben shugaban kasa.

Obi ya ƙi ya rungumi kaddarar rashin nasara, ya kalubalanci nasarar Tinubu a babban zaben da aka kammala ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023.

Kara karanta wannan

"Allah Ne Ya Cece Mu" Gwamna Arewa Ya Tona Ainihin Dalilin Da Yasa Gwamnoni Suka Goyi Bayan Tinubu

Ya nemi Kotu ta soke zaben Tinubu kuma ya gabatar da buƙatar ta sahalewa kafafen watsa labarai su haska zaman sauraron karar kai tsaye, Within Nigeria ta rahoto.

Abbas da Zababbun Yan Majalisar Tarayya Sun Gana da Shettima

A wani labarin kuma Ɗan Takarar Kakaki da Yan Majalisun APC da PDP Sun Sa Labule da Mataimakin Tinubu

Abbas Tajudden da tawagar zababbun yan majalisar wakilan tarayya ta 10 sun ziyarci zababben mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima.

Taron jiga-jigan jam'iyyar APC ya samu halartar gamayyar yan majalisun tsagin Adawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel