"Na Taki Sa'ar NYSC": Mace Mafi Gajarta Za Ta Auri Dan Bautar Kasa Mafi Tsawo A Sansaninsu, Hotunansu Sun Yadu

"Na Taki Sa'ar NYSC": Mace Mafi Gajarta Za Ta Auri Dan Bautar Kasa Mafi Tsawo A Sansaninsu, Hotunansu Sun Yadu

  • Wata mata yar Najeriya mai kankanin jiki ya bada labarin soyayarta a Facebook yayin da ta ke shirin aure
  • A cewar matar mai cike da farin ciki, ta hadu da sahibinta ne a sansanin horas da masu yi wa kasa hidima, NYSC
  • Matar ta bayyana cewa da farko dai sun fara ne da abota a yayin da abokai suke yawan magana kan banbancin tsawonsu

Wata mata yar Najeriya, Innocent Ruth, ta yi fice a dandalin sada zumunta bayan ta sanar da cewa ta hadu da wanda za ta aure a sansanin horas da yan gudun hijira na NYSC.

Matar mai kankanin jiki ta bayyana cewa ta hadu da saurayin da za ta aura, mai tsawo sosai a sansanin horas da yan NYSC kuma suka zama abokai.

Mai tsawo da gajeruwa
Yan yi wa kasa hidima za su yi aure. Hoto: @Innocent Ruth
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

"Ya Yi Wuff Da Tsaleliyar Budurwa": Yadda Hoto Da Bidiyon Wani Ango Da Ya Wuff Da Kyakkyawar Yarinya Ya Haddasa Cece-Kuce

A cewar ta, an basu lambar yabo na mai tsawo da mafi gajarta a tsakanin yan yi wa kasa hidimar. Amma, bayan wani dan lokaci sai suka shaku kuma suka fara soyayya har ya nemi ta aure shi kuma ta amsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rubutun da ta yi a shafin sada zumunta ya dauki hankulan mutane sosai wadanda galibi banbancin tsawonsu ya burge su.

Masu amfani da intanet kuma sun jinjina musu bisa kwarin gwiwar cigaba da soyayya duk da banbancin tsawonsu.

Ga abin da ta rubuta a Facebook.

"Mun hadu a sansanin horaswa ta NYSC, dama ashe sa'a na taka a sansanin? Mun zama abokai kuma sauran ya zama tarihi. Dan NYSC mafi tsawo da mafi gajarta. Ina taya mu murna."

Ga wallafar a kasa:

Martanin masu amfani da shafukan sada zumunta

Kara karanta wannan

Budurwa Ta Koka Yayin da Ta Ci Karo Da Mahaifiyarta Tana Karanta Hirarta Da Saurayinta a WhatsApp, Bidiyon Ya Yadu

@Joseph Omamode ya ce:

"Ina taya ku murna, amma mata ba su tsoro fa, ta yaya za su yi inda za su yi sumbata."

@Emmanuel Ebga cewa ya yi:

"Bayelsa batch B1 2021."

@Alhaji Power ya rubuta:

"Barka, wannan shine ake kira soyayya na nesa."

@Innocent Enang Ererra ya ce:

"Wane irin tsawo ne wannan."

@Rita Ezinna cewa ta yi:

"Ina taya ku murna."

@Oge Chukwu ta yi martani kamar haka:

"Da kyau!, Ina taya ku murna!"

Wata mace ta bar wani saurayi ya jingina a jikinta, hotunan su sun dauki hankulan mutane

Wata budurwa yar Najeriya mai suna @Sweet_cocolatey a shafin Twita ta wallafa wani hoto da ke nuna haduwarta da wani fasinja na miji a cikin motar haya.

A rubutun da ta yi a ranar Juma'a 2 ga watan Disamba na 2022, ta ce saurayin ya dan jingina ya kwanta a jikinta kuma ba ta damu ba.

Kara karanta wannan

Wasa Da Rai: Bidiyon Wata Kyakkyawar Budurwa Cikin Zakuna Ya Janyo Cece-Kuce

Asali: Legit.ng

Online view pixel