Mummunan Karshe: Dan Ta’adda Ya Kai Kansa Ziyara Barzahu Garin Fafatawa da DSS

Mummunan Karshe: Dan Ta’adda Ya Kai Kansa Ziyara Barzahu Garin Fafatawa da DSS

  • Wani wanda ake zargin dan ta’adda ne ya ciyar da kansa taliyar karshe a duniya saboda gudun kada a kama shi a jihar Kaduna
  • Mutumin da ake zargin yana da kayayyakin fashewa a jikinsa lokacin da jam’ian tsaro suka yiwa gidansa kawanya
  • Bayan mutuwarsa, jami’an farin kaya sun kama matarsa da ‘ya’yansa suka tafi da su a cikin motarsu zuwa ofishinsu

Jihar Kaduna - Wani wanda ake zargin dan ta'adda ne da yake dauke da kayayyakin fashewa a jikinsa ya mika kansa madakata saboda gudun kada a kama shi.

Lamarin ya faru ne a hanyar Ibrahim Haske a gundumar Keke dake cikin garin Kaduna a ranar Litinin 15 ga watan Mayu.

jami;an farin kaya/ sojoji
Yadda Dan Ta’adda Ya Kashe Kansa Bayan Artabu da Jami’an Farin Kaya da Sojoji a Kaduna, Hoto: Daily Post
Asali: Facebook

Shaidan gani da ido ya tabbatar da cewa an jiyo harbe-harben bindigogi da misalin karfe 1 na dare lokacin da jami’an farin kaya da sojoji da kuma ‘yan sanda suka zo kama wanda ake zargin.

Kara karanta wannan

Buhari Ba Shi da Asusun Banki Ko Daya Dake Shake da Kudin Haram, in Ji Garba Shehu

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa lokacin da mutumin ya fahimci an yi wa inda yake kawanya, sai yayi amfani da wannan daman ya tada kayan fashewar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Artabu tsakaninsa da jami'an farin kaya da sojoji

Rahotanni sun tabbatar da cewa sunyi artabu sosai da jami’an tsaron kafin daga karshe ya kai ziyara barzahu.

Wata majiya ta jami’an tsaro ta bayyana cewa an samu bindiga kirar AK-47 a cikin gidan da kuma wasu abubuwan fashewa wadda daga baya jami’an kunce bam suka lalata shi.

Wani mazaunin unguwan kuma wanda ya kasance shugaba a yankin, Mallam Sama’ila ya tabbatar da faruwan lamarin inda yace jami’an tsaro sun tare mashigar gidan mutumin.

Yadda aka gano inda mutumin yake

Ya kara da cewa zai iya yiyuwa jami’an tsaron sun yi amfani da na’ura ne wurin gano inda mutumin yake don su kama shi.

Kara karanta wannan

Wasu Wurare 4 da Bola Tinubu Zai Iya Shan Wahala Bayan Ya Gaji Muhammadu Buhari

Bayan mutumin ya fahimci babu wata hanyar tsira sai yayi tunanin cewa ga garinku nan da abubuwan fashewa a cikin gidan.

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Muhammad Jalige bai amsa wayarsa ba kuma bai maida martanin sakon kar ta kwana da aka tura masa ba.

Sojoji Sun Gano Wani Makeken Rami Da Aka Birne Makamai Masu Dimbin Yawa A Sambisa

A wani labarin, rundunar hadin guiwa ta sojoji a jihar Borno ta gano wani makeken rami dauke da muggan makamai a dajin Sambisa.

Rundunar ta ce ta gano ramin ne bayan samame ta suka kai a yankin tare da bayyana makamai dake cikin ramin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel