"Ba Ya Cin Hanci Da Rashawa": Turai ’Yar Adua Ta Siffinta Halin Mijinta Shekaru 13 Bayan Mutuwarsa

"Ba Ya Cin Hanci Da Rashawa": Turai ’Yar Adua Ta Siffinta Halin Mijinta Shekaru 13 Bayan Mutuwarsa

  • Matar marigayi tsohon shugaban kasar Najeriya, Hajiya Turai Yar Adu'a ta ce mijinta ba dan rashawa ba ne, kowa ya sani
  • Turai ta kara da cewa mijinnata ba ya neman mata kuma ba ya shan giya, inda tace mutumin kirki ne mai kaunarta da gaske
  • Ta bayyana marigayin a matsayin mutumin kirki wanda bai dauki rayuwar duniya komai ba kuma mai son kwanciyar hankali

Jihar Katsina - Matar tsohon shugaban kasan Najeriya, Turai ‘Yar Adua ta ce mijinta marigayi Alhaji Umaru Musa ‘Yar Adua ba ya cin hanci da rashawa.

Turai ta bayyana hakan ne a cikin wata hira ta musamman da kafar labarai ta BBC Hausa a ranar jimamin zagayowar mutuwar tsohon shugaban kasan na Najeriya.

Idan baku manta ba, Allah ya yi wa Yar Adua rasuwa a ranar 5 ga watan Mayun 2010, inda Najeriya da sauran kasashen makwabta da ke mutunta shugaban suka jimami da alhinin rashi.

Kara karanta wannan

Na Tuba: Budurwar Da Ke Tallan Kanta Da Hotunan Batsa Ta Tuba, Ta Mika Rayuwarta Ga Addini

Turai ta ba da labarin Yar Adua
Hajiya Turai 'Yar Adua, matar tsohon shugaban kasa | Hoto: TVC News
Asali: Facebook

Mijina mai saukin kaine, inji Turai

Da take zantawa da BBC Hausa, ta ce tabbas mijinta ba dan rashawa bane, kuma duniya ma ta shaida hakan.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da take siffanta saukin kai da gudun duniya irin na mijin nata, cewa ta yi:

“Shi dai mutum ne mai saukin kai, bai dauki duniya a matsayin komai ba, gaskiya saboda zai iya sanya agogo a hannunsa har sai ledar agogon ta rabu biyu.”

Mijina ba dan rashawa bane

Ta kuma bayyana siffofin mijinta a lokacin da take bai wa sabuwar uwar gidan shugaban kasar Najeriya shawari kan tafiyar da mulki, inda ta ce:

“Mijina bai shan giya, mijina bai neman mata, mijina ba ya cin hanci da rashawa, don haka idan za a bashi haushi sai ace yana son matarsa.”

Turai ‘Yar Adua Ta Tuna da Zantawarta ta Karshe da Marigayi Shugaba ‘Yar’adua

Kara karanta wannan

"Ba Ka Bi Na Bashin Komai": Wasu Muhimman Abubuwa 5 Da Tinubu Ya Fada Yayin Da Wike Ya Gayyace Shi

Hajiya Turai Yar Adu'a, Matar marigayi tsohon shugaban kasar Nijeriya, ta yi bayanin ganawarta ta karshe da marigayin a lokacin da ya ke fama da jinya.

Turai ta yi wannan bayani ne lokacin da ake jira da ita da gidan jaridar BBC Hausa, in da tace kullum a cikin tuna marigayin ta ke.

Ta ce shi mutum ne da ya kasance ba ya rashawa, neman mata ko shan giya, sai dai abun da ta sani ya na sonta sosai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel