Turai ‘Yar’adua Ta Tuna da Lokacin Karshe da Marigayi Shugaba ‘Yar’adua a Aso Rock

Turai ‘Yar’adua Ta Tuna da Lokacin Karshe da Marigayi Shugaba ‘Yar’adua a Aso Rock

  • Turai ‘Yar’adua ta bayyana Umaru Musa ‘Yar’adua a matsayin mutumin da bai damu da Duniya
  • Tsohuwar uwargidar Najeriya ta bada labarin ganin karshe da tayi wa Marigayin kafin ya bar Duniya
  • Hajiya Turai ta ce saboda a fusata ‘Yar’adua ne aka rika yi mata sharri a lokacin da suke Gwamnati

Abuja - A wata hira da aka yi da Turai ‘Yar’adua a gidan BBC Hausa, tayi bayanin halin da ta shiga da kuma yadda rayuwa ta ke a yau bayan rasa mai gida.

An zanta da tsohuwar shugabar Najeriyar ganin a makon nan Umaru Musa ‘Yar’adua ya cika shekaru 13 da rasuwa, ta ce ita kullum cikin tuna mijinta take yi.

A wajen Hajiya Turai ‘Yar’adua bambancin rana irin ta 5 ga watan Mayu da sauran ranaku shi ne mutane su na yi wa tsohon shugaban kasar addu’o’in gafara.

Kara karanta wannan

'Yan Sanda Sun Cafke Matashi Da Ya Halaka Mahaifiyarsa a Kano

Da aka nemi jin lokacinta na karshe da tsohon shugaban na Najeriya, sai ta ce a lokacin ta na azumi kamar yadda ta saba tun da ya kamu da cutar ajalinsa.

Kamar yadda ta fada, a lokacin ta shirya za ta tafi yin buda baki, sai ‘Yar’adua ya nuna bai so ta bar wurinsa, tafiyarta ke da wuya sai ya shiga magagin mutuwa.

Turai ta bar wa Allah SWT komai

Ko a lokacin da Turai ‘Yar’adua ta dawo, sai ta iske numfashin mai gidanta yana daukewa, har tayi nadamar tafiya shan ruwan, ta ce dama ba ta je ko ina ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A matsayinta na Musulma, tsohuwar uwargidar kasar Najeriya ta ce ta rungumi kaddara domin Allah (SWT) ne ya karbi mijinta bayan baiwar da ya yi masu.

Turai Yar'Adua
Hajiya Turai ‘Yar’adua da Marigayi Shugaba Umaru ‘Yar’adua Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Tsohon gwamna Umaru Musa ‘Yar’adua mutum ne mai matukar saukin-kai wanda bai damu da Duniya ba, Turai ta ce sam mijinta bai da kwadayin shugabanci.

Kara karanta wannan

Kujerar Kakaki: Ado Doguwa Ya Ce Mata 4 Da 'Ya'ya 28 Yake Dashi, Zai Iya Ji da Majalisa

A zantawar da aka yi da ita, Turai ta ce mijin na ta zai iya daura agogo daya a hannunsa har sai agogon ya yi fata-fata, har sai ta lura da hakan, ta canza masa.

'Yaradua yana kaunar Turai

Har gobe kuwa wannan Baiwar Allah ta ce a farin ciki ta ke a dalilin irin kaunar da Marigayin ya nuna mata, har ta rasa mai gidanta tamkar amarya take a gidansa.

Ko da ta ke fadar gwamnati, Turai ta ce ta na yin girki, da zarar tayi tafiya zuwa wani wuri, ‘Yar’adua yake fara kiranta a waya domin jin ko ta sauka masauki lafiya.

Bayan ta rasa sahibi, sai tayi tafiya wata rana, ko da ta isa sai ta ji babu wanda ya kira ta a waya, a nan ta ce ta sharara kuka na rashin mahaifin ‘ya ‘yanta a Duniya.

Turai ta ba Remi Tinubu shawara ta zama mai hakuri domin za a rika yi mata sharri kamar yadda aka yi mata saboda an lura tsohon shugaban kasar yana kaunarta.

Kara karanta wannan

Karya kike: Bidiyon yadda yarinya ta fashe da kukan haushin ta ci maki 259 a JAMB

Addu'o'i na musamman

Kamar yadda rahoto ya zo a baya, Umaru Musa 'Yar'adua ya cika shekara 13 da rasuwa, amma da alama har yau mutane ba su manta da tsohon shugaban ba.

Katsinawa da 'ya'yan jam'iyyar PDP sun gudanar da addu'o'i Allah ya ƙara kai haske ƙabarinsa. Kafin zamansa shugaban kasa, 'Yar'adua ya yi Gwamna a Katsina.

Asali: Legit.ng

Online view pixel