Yadda Allah Ya Taimake Ni Na Haddace Alkur'ani Bayan Na Musulunta, Zainab

Yadda Allah Ya Taimake Ni Na Haddace Alkur'ani Bayan Na Musulunta, Zainab

  • Wata baiwar Allah da ta Musulunta ta bayyana yadda ta haddace Alkur'ani tun daga farko har ƙarshe
  • Zainab ta kuma bayyana yadda ta karbi Shahada daga zuwa ziyara wurin wata yar uwarsu a Najeriya
  • Mahaifinta ɗan ƙasar Ghana ne kuma a can take zaune amma mahaifiyarta yar Najeriya ce a jihar Kogi

Rejoice Afebli wacce ta sauya sunanta zuwa Rejoice Zainab bayan ta bar Kiristanci ta karbi addinin Musulunci, ta labarta yadda ta haddace littafi mai tsarki Alƙur'ani.

Zainab, wacce ta koma sanya Niƙabi bayan ta musulunta, ta shaida wa Daily Trust cewa an haifeta a gidan mabiya addinin Kirista, mahifinta Michael Afebli, ɗan ƙasar Ghana ne, mahaifiyarta kuma yar Najeriya.

Rejoice Zainab
Yadda Allah Ya Taimake Ni Na Haddace Alkur'ani Bayan Na Musulunta, Zainab Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Ta ce mahaifiyarta, Misis Mrs Otaru Aina Florence, yar garin Ogaminana, ƙaramar hukumar Adavi da ke jihar Kogi, arewa ta tsakiya a Najeriya.

Kara karanta wannan

Faragaba Ta Ƙaru, Hukumar Sojin Najeriya Ta Fallasa Masu Hannu a Shirin Hana Rantsar da Bola Tinubu

Me ya ja hakin Rejoice ta karɓi Musulunci?

Zainab ta bayyana cewa suna da yan uwa Musulmai amma suna da nisa amma Iyayenta Kiristoci ne na sahun gaba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta ce ta karbi addinin Musulunci yayin da ta kawo ziyara Najeriya bayan ta kammala karatun Sakandire tana jiran samun Admishin zuwa Jami'a.

"Na zo Najeriya domin na taimakawa ƙawata ta danginmu a shagon siyar da magunguna saboda ina ƙaunar karatun Likita. Amma ban san Allah ya tsara zan Musulunta ta dalilinta ba."
"Ina ƙaunar matar da iyalan gidansu saboda kyawawan halayenta da yaranta, suna shiga ta kamala. Daga nan na fara sha'awar sanin Addinin Musulunci bayan wani lokaci na gamsu."

Zainab ta bayyana cewa ta gode wa Allah SWT saboda ta karbi shahada kafin ta samu takardar shaidar shiga jami'a a ƙasar Ghana."

Yadda na haddace Alkur'ani - Rejoice Zainab

Kara karanta wannan

Innalillahi: Matashin Saurayi Ya Burma Wa Mahaifiyarsa Wuƙa Har Ta Mutu a Kano

Zainab ta ce bayan ta shiga jami'ar Cape Coast a Ghana domin ta karanta Likitanci a 2015, sai Allah ya haɗata da wasu ɗalibai mata biyu, ɗaya ta haddace Alƙur'ani, ɗayar kuma ta haddace fiye da rabi.

"Hakan ya ƙara mun kwarin guiwa, har na fara ƙosawa na rika sanya tufafi irin nasu duk da ban yi zurfi a ilimin Musulunci ba, amma ina bakin kokarina kuma na kan sanya Niƙabi."
"Lokacin ina Ghana, na haddace daga Sura ta 58, Suratun Mujadalah zuwa Nasi shafi 62 kenan ba tare da na san baƙin larabci ko ɗaya ba, na haddace ne ta hanyar sauraron karatun da kokarin bin muryar mai karatun."
"Da na zo Najeriya na dawo farko, inda na haɗu da wani Malami Ustaz ya koyamun littafin koyon larabci Nurul Bayan. Yanzu na haddace Alkur'ani a makarantar Assunnah Academy of Arabic and Islamic Studies,Tanke, Ilọrin."

A wani labarin kuma Yadda Al'ummar Jihar Katsina da wasu jiga-jigan PDP suka gudanar da taron Addu'o'in tunawa da Yar'Adua.

Kara karanta wannan

Tinubu, Atiku Ko Obi? Tsohon Shugaban Kasa Ya Roki Alfarma 1 Wurin Yan Najeriya Kan Shari'ar Zaben 2023

Ranar Jumu'a 5 ga watan Mayu, 2023, tsohon gwamnan Katsina kuma tsohon shugaban ƙasa, Umaru Musa Yar'adua ya cika shekaru 13 da rasuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel