“Ruwa Ya Hargitsa Komai”: Matashiya Ta Koka Yayin da Ruwan Sama Ya Cike Filin Bikinta a Bidiyo

“Ruwa Ya Hargitsa Komai”: Matashiya Ta Koka Yayin da Ruwan Sama Ya Cike Filin Bikinta a Bidiyo

  • Wata matashiyar budurwa ta wallafa bidiyon da ke nuna yadda ruwan sama kamar da bakin kwarya ya lalata wajen shagalin bikinta
  • Bidiyon da aka wallafa a ranar 3 ga watan Mayu ya nuna cewa ruwan saman ya fara ne jim kadan bayan an gama kawata wajen bikin
  • Sai dai kuma, an yi bikin daga baya kuma mutane sin ce ruwan saman na iya zama alkhairi ga budurwar da mijinta

Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya tarwatsa harkoki yayin sha'anin wani bikin aure kamar yadda aka gani a wani bidiyon TikTok.

Amaryar da kanta ce ta wallafa bidiyon a shafinta na TikTok mai suna @sasha40405.

Amarya da wajen biki cike da ruwan sama
“Ruwa Ya Hargitsa Komai”: Matashiya Ta Koka Yayin da Ruwan Sama Ya Cike Filin Bikinta a Bidiyo Hoto: @sasha40405
Asali: TikTok

Ruwan saman ya fara ne jim kadan bayan an gama kawata wajen bikin kuma ana gab da fara shagali.

Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya tarwatsa taron biki

Kara karanta wannan

“Ba Zan Iya Bacci Ni Kadai Ba”: Uwa Ta Bude Kofar Daki, Ta Gano Diyarta Kwance a Gadon Kaninta, Mutane Sun Bata Shawara

A bidiyon, an gano gaba daya wajen ya yi kaca-kaca da ruwan kwatami.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ruwan saman ya kuma jika abubuwa da dama da aka yi amfani da su wajen kawata wajen bikin.

An gano mahalarta bikin suna samun mafaka a karkashin manyan lema da aka daura a wajen wadanda iska ya dunka kadasu tare da cire wasun su.

Sai dai kuma, amaryar ta ce an yi bikin duk da ruwan saman da aka yi. Ta ce ruwan saman ya so bata mata rana, amma bai cimma nasara ba.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@Kesterblings ta ce:

"Yan lokaci na damuna su duba yiwuwar kama dakin taro ko su jira har zuwa watan Satumba.

@Asawan ta ce:

"Wannan ruwan albarka ne ki je ki ji dadin aurenki sannan ki tafi gida da sunan Allah."

Kara karanta wannan

Bani da ko saurayi: Budurwa ta ce tallan gwanjo na kai mata, ta sayi motar N36m

@Azike Ngozi cta yi martani:

"Ku daina biki a lokacin idan ba za ku iya aron dakin taro ba."

@Realesi4life ta ce:

"Ki yi addu'a sannan ki godewa Allah saboda ya albarkaci aurenku."

@idara ta ce:

"Idan da ni ce, da na fashe da kuka."

Matashiya ta koka bayan mahaifiyarta ta ziyarceta, ta ce tana kokarin kashe mata aure

A wani labarin kuma, wata matashiya ta shiga tasku bayan mahaifiyarta ta kai mata ziyara a gidan aurenta. Mijinta dai baya so wani daga cikin danginta ya rabeta don haka ya dungi fushi da ita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel