“Mahaifinmu Daya”: Matashi Ya Gano Cewa Budurwar Da Ya Yi Wa Ciki Kanwarsa Ce

“Mahaifinmu Daya”: Matashi Ya Gano Cewa Budurwar Da Ya Yi Wa Ciki Kanwarsa Ce

  • Zuciyar wani matashi dan Najeriya ya karaya bayan ya gano cewa budurwarsa da ya yi wa ciki kanwarsa ce ta jini
  • Matashin ya yi tattaki har zuwa Amurka inda ya hadu da matar sannan ya yi mata ciki
  • Bayan ya nemi haduwa da iyayenta, sai ya gano cewa mahaifinta shine mahaifinsa shima

Labarin wani matashi dan Najeriya wanda ya gano cewa mahaifin budurwarsa shine uban da ya haife shi shima ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya.

A cewar labarin wanda @KhJrSly ya wallafa a Twitter, matashin ya koma Amurka da zama ne inda ya hadu da sahibarsa.

Hoton wani mutum da na wasu matasa
“Mahaifinmu Daya”: Matashi Ya Gano Cewa Budurwar Da Ya Yi Wa Ciki Kanwarsa Ce Hoto: @FG Trade
Asali: Getty Images

Bayan sun yi soyayya na dan lokaci, sai ya yi mata ciki sannan ya yanke shawarar haduwa da iyayenta domin yin wasu yan shirye-shirye.

Abun bakin ciki, da isarsa gidan, sai ya gano cewa mahaifin yarinyar ai ubansa ne shima.

Kara karanta wannan

“Wayyo Allah Ni Cokali Ce?” Bidiyon Kyautar Tsaleliyar Mota Da Saurayi Ya Yi Wa Budurwarsa Ya Dauka Hankali

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na nufin, mutumin yana da wata matar a waje wanda shine ya kai ga haihuwar wannan yarinyar wanda babu wanda ya sani.

Matashin ya zauce sannan ya fara fama da lalaurar tabin hankali tun daga lokacin.

"Mahaifiyarka ce kadai ta tayar da kai, ka yi wa budurwarka ciki a Amurka. Sai ta kai ka gida don haduwa da iayayenta sannan mahaifinta shine mahaifinka da ya haifeka. Mutumina na fama da tabin hankali a yammacin nan", yadda labarin ya zo.

Jama'a sun yi martani

Chief Desmond ya ce:

"Karamin duniya amma na rantse za mu manta da zancen uwa da uba ne sannan mu je mu yi rayuwarmu tare."

Mawutor ta rubuta:

"Duk tsawon lokacin da suka dauka suna soyayya bai san iyayen budurwar ba?"

Big Striker ya yi martani:

"Wai duk ba kwa tambayan masoyanku daga inda suke ne? Su wanene iyayenku ko wani abun."

Kara karanta wannan

“Uba Ya Kasa Shanye Hawayensa”: Matashi Ya Fashe Da Kuka Shabe-Shabe Yayin da Diyarsa Ta Amarce

Manny Frimps ta rubuta:

"Abun bakin ciki ne cewa a kullun yara ne kadai ke biyan bashin laifukan da iyayensu suka yi."

Kalli wallafar a kasa:

Matashiya ta shiga tasku bayan mahaifiyarta ta ziyarce ta a gidan miji, bata son zuwanta

A wani labarin, wata matashiya ta shiga tsaka mai wuya bayan da mahaifiyarta ta kai mata ziyarar bazata gidan mijinta.

Tun daga lokacin mijin ya juya mata baya domin ya gargadeta a kan baya son kowani dan uwanta ya rabe su, ta nemi mahaifiyar ta tafi amma ta yi biris.

Asali: Legit.ng

Online view pixel