Da So Samu Ne, a Samu Jirage 4 Su Yi Zuwa Daya Su Kwaso ’Yan Najeriya Daga Sudan Kowa Ya Huta

Da So Samu Ne, a Samu Jirage 4 Su Yi Zuwa Daya Su Kwaso ’Yan Najeriya Daga Sudan Kowa Ya Huta

  • Gwamnatin Najeriya ta ce akwai bukatar karin jirage hudu domin kwaso ‘yan Najeriyan da suka makale a Sudan
  • Ana ci gaba da tattaro ‘yan Najeriyan da yaki ya rutsa dasu a Sudan, inda da yawa suka yi hijira zuwa Masar
  • A jiya, an tattaro mutum 350 da aka ce sun galabaita a kasar, inda suka samu kyautar kudi daga gwamnati

FCT, Abuja - Gwamnaton Najeriya ta ce, idan da za a samu jiragen sama hudu, zuwa daya za a yi wajen kwaso dukkan daliban da suka makale a kasar Sudan da ke fama da rikici.

Rukunin farko na ‘yan Najeriyan da suka makale a Sudan tuni aka dauko su a jiya Laraba, inda aka sauke su a filin saukar jiragen sama da ke Abuja, Vanguard ta ruwaito.

A cewar hukumomin Najeriya, shirin tattaro ‘yan Najeriya da ke kasar zai kai mutum 3,500, amma akwai yiwuwar sun fi haka gidan aka hada da dalibai da wadanda ke rayuwa a can.

Kwaso 'yan Najeriya na zuwa da matsala
Yadda aka kwaso 'yan Najeriya daga Sudan | Hoto: @abikedabiri
Asali: Twitter

Jirgin kasuwanci na Najeriya, Air Peace ya sauka a jiya da misalin karfe 11:40 na dare dauke da mutane 260, yayin da jirgin sojin sama kuma ya dauko mutum 94.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da so samu ne, a samu karin jirage 4 su kwaso ‘yan Najeriya daga Sudan

A bangare guda, shugaban hukumar kula da ‘yan Najeriya mazauna waje (NiDCOM), Abike Dabiri Erewa ta ce da za a samu karin jirage hudu da an rage aiki.

A cewarta, idan akwai karin jirage hudu, zuwa daya za a yi wajen kwaso ‘yan Najeriyan da suka makale a kasar ta Sudan, rahoton Punch.

Ta bayyana hakan ne a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja yayin da ake jiran saukar ‘yan Najeriyan da aka dauko daga Masar.

A cewarta, a yanzu haka, ana tsammanin kwaso ‘yan Najeriyan da suka makale akalla 3,000.

Ta kuma shaida cewa, gwamnatin Masar na ci gaba da nuna bukatar a turo jirage domin kwashe ‘yan Najeriya da ke cikin kasar wadanda suka yi hijira daga Sudan.

An raba wa ‘yan Najeriyan da aka kwaso daga Sudan kudi

A bangare guda, rahoto ya bayyana yadda aka raba wa ‘yan Najeriyan da aka kwaso daga Sudan kudi a filin jirgin Najeriya.

Kudin na zuwa ne ta ma’aikatar jin kai da walwala, inda aka ce Dangote ne ya ba da kudin a basu.

Hakazalika, an ce kamfanin MTN ya ba ‘yan Najeriya katin waya na N25,000 da kuma data 1.5GB duk dai a lokacin da suka sauka a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel