“Rashin Hankali”: Wani Mutum Ya Fasa Auren Budurwarsa Bayan Gani Ta Kai Ziyarar Karshe Ga Tsohon Saurayinta

“Rashin Hankali”: Wani Mutum Ya Fasa Auren Budurwarsa Bayan Gani Ta Kai Ziyarar Karshe Ga Tsohon Saurayinta

  • Wani dan Najeriya ya soke aurensa bayan da ya gani budurwarsa ta kai ziyarar karsje ga tsohon saurayinta
  • Bayan rabuwarsu, budurwar ta dauko batun zuwa wani dakin kafar sada zumunta domin neman shawarin jama’a
  • Ta kuma amsa laifinta cewa, tabbas ta rakashe tare da tsohon saurayinta, kawai ta yi rashin sa’a wanda zai aure ta ya gane

Wata budurwa ‘yar Najeriya ta shiga kunci yayin da saurayin da za ta aure ya ce sam ya fasa, ya soke aurensu.

A cewar wani bidiyon da ya yadu a kafar Faccebook, mutumin da zai auri budurwar ya gano yadda ta kai ziyarar karshe wurin wani tsohon saurayinta.

Budurwar, wacce ba a bayyana sunanta ba ta bayyana yadda lamarin ya faru a dakin kafar Facebook, inda ta nemi jin ra’ayoyin jama’a game da lamarin.

Kara karanta wannan

"Yana Iya Zautar Da Mutum": Yadda Matar Aure Ta Ci Amanar Mijinta Na Sunnah, Sam Ba Ta Yi Da Na Sani Ba

Saurayi ya fasa auren budurwarsa
Aure ya fasu saboda abu daya | Hotuna: Jasmin Merdan, Luis Alvarez and Anna Ivonina (Hotunan nan ba na gaskiyar mutanen da lamarin ya faru dasu bane, an buga misali ne dasu)
Asali: Getty Images

Dalilin da yasa ta je gidan tsohon saurayinta

A cewarta, ta ziyarci tsohon saurayinta ne domin kai masa katin gayyatar aure, amma aka samu matsala suka aikata badala.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta kuma bayyana cewa, da gaske akwai laifinta, amma bata je da niyyar yin lalata da tsohon saurayin ba.

Ta rashin sa’a, domin kuwa mijin da za ta aure ya gano komai bayan da ya datsi manhajar fira ta WhatsApp da budurwar ke amfani ita.

Daga nan, sai kawai mutumin ya ce ya soke duk wani shiri na auren ba tare d abata lokaci ba, ya ma fasa aurenta.

Ya hada ni da iyaye, inji budurwar

Labarin da ya fito ne daga bangarori daba yawa na Facebook, inda ake sake yada shi da jin mamaki.

Ta ce:

“A gaba na, ya kira dukkan iyayenmu sannan ya nemi a soke duk wani shirin auren. Lokacin da suka nemi sanin dalili, yace musu zan fi musu bayani da kyau. A nan ya bar ni cikin gidansa ya tafi wani otal kuma Abuja zai koma daga otal din.”

Kara karanta wannan

"Duk Da Na Mallaki Kwalin Digiri Biyayyar Aure Zan Yi" - Matashiya Ta Bayyana a Bidiyo

Martanin jama’a a Facebook

Kingsley Uchenna:

“Rashin hankali. Meye yasa kika karbi dan wani bayan kinsan kina son tsohon saurayinki? Wannan rayuwar EEE. Mutumin ya yi daidai. Ya yi imanin za ki yi abin da ya fi haka bayan aurenku.

@Adeoye Augustine Okusanya:

“Meye yasa kika mai da wulakanta kanki haka? Kamar dai har yanzu kina son tsohon saurayinki.”

Ba sabon abu bane samun matsala a gidan aure ko kuma tsakanin ma'aurata, wasu suna yi fada ne a kan kudi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel