Ministan Kwadago, Ngige, Ya Bayyana Ainihin Albashinsa, Ya Ce Bashi Da Wani Alawus, Duba Bidiyon

Ministan Kwadago, Ngige, Ya Bayyana Ainihin Albashinsa, Ya Ce Bashi Da Wani Alawus, Duba Bidiyon

  • Ministan kwadago, Chris Ngige, ya ce albashin ministoci ₦942,000 ne, kuma ba a biyansu alawus
  • Ngige ya ce alawus din ziyarar aiki kawai ake basu kamar yadda ake baiwa kowane ma'aikaci
  • Ministan ya kuma alakanta rashin aikin yi da karancin zuba hannun jari daga kasashen waje

Biyo bayan kiraye-kirayen da ake na a kara mafi karancin albashi daga ₦30,000, ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Dakta Chris Ngige, ya bayyana cewa albashinsa da na sauran ministoci ₦942,000 ne wata bayan sun biya haraji.

Ngige, wanda ya bayyana haka a shirin Siyasa a Yau ta Channels TV ranar Litinin, ya kuma ce ba a biyansu alawus saboda an daina biyan alawus din tafiye tafiyen aiki.

Ministan Kwadago, Ngige
Ministan Kwadago, Ngige, Ya Bayyana Ainihin Albashinsa, Ya Ce Bashi Da Wani Allawus, Duba Bidiyon. Hoto: Chris Ngige
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

2023: Makaho ne kadai zai ce Tinubu ya ci zabe, LP ta yiwa APC wankin babban bargo

Albashina N942,000 ne kacal, Ministan Buhari, Chris Ngige

''Albashina ₦942,000 a wata. Albashina da na mai taimaka min - jimilla idan an cire haraji- kudin abinci, tafiye tafiye nawa da na mataimakina, albashin mai kula da tsirrai, mai dafa min abinci, duk a hade yake. Bayan zaftare haraji, ana biyana ₦942,000.
"Duk wani minista da ka gani, haka ake biyansa; mashawarta na musamman su ma kusan haka ake biyansu. Babu wani alawus, ba wani alawus in dai ba tafiya zaka yi ba. Za a baka kudin ziyarar aiki kamar sauran kowane ma'aiki," in ji Ngige.

Ya ce kudin tafiye tafiye ma sai da aka sake nazarinsa tare da na manyan sakatarorin ma'aikatu da ma wasu da dama.

"An yanke za a dinga biyan minista ₦100,000, karamin minista, ₦75,000; manyan sakatarori, ₦70,000, haka abin ke raguwa. Daki daki, an sake duba na kowa," in ji shi.

Kara karanta wannan

Atiku ne ya lashe zabe: PDP ta caccaki ministan Buhari, ta tono barnar APC

Daukan Ma'aikata Alhakin Masana'antu Masu Zaman Kansu Ne, Ngige

Da aka tambaye shi dalilin da ya sa har yanzu gwamnati ta kasa rage yawan rashin aikin yi a kasar, wanda ya karo zuwa kaso 33.3 a 2021, Ngige ya ce samar da ayyukan yi alhakin masana'antu masu zaman kansu ne ba iya na gwamnati ba.

Ya kuma zargi rashin zuba hannun jari daga kasashen waje a matsayin abin da ke jawo karuwar rashin aikin yi.

"Batu na gaskiya shi ne batun samar da aikin yi ya ci tura; ba iya alhakin gwamnati ba ne," in ji Ngige.
"Kowa na ganin laifin gwamnati ne rashin aikin yi: idan ba mu yi aiki a ma'aikatar gwamnati ba to ba mu samu aiki ba.' A'a akwai masana'antu masu zaman kansu."

Ministan ya yi bayani cewa masana'antu masu zaman kansu na da guraben da za su samar da ayyukan yi ta fannin noma da sauran bangarori.

Kara karanta wannan

Yaki ake: FG ta fadi dalilin da yasa dauko 'yan Najeriya daga Sudan zai ci $1.2m

"Ba iya gwamnati abin ya shafa ba. Kuma ina fada maka yanzu, idan tattalin arziki ba shi da kyau, ba za a samu isassun kudi da za su samar da ayyukan yi ba. Wannan shi ne matsalar; babu masu zuba jari daga kasashen waje," a cewarsa.

FG Za Ta Yi Wa Ma'aikatan Najeriya Karin Albashi A Watan Afrilu

A wani labarin, gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce ma'aikata za su samu karin albashi a watan Afrilu.

Gwamnatin ta ce ma'aikatan za su fara karban sabon albashin ne gabanin cire tallafin man fetur da ake fatan yi a kasar nan ba da dadewa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel