Makaho Ne Zai Yarda da Sakamakon Zaben Shugaban Kasa Na 2023, Martanin LP Ga Lai Mohammed

Makaho Ne Zai Yarda da Sakamakon Zaben Shugaban Kasa Na 2023, Martanin LP Ga Lai Mohammed

  • Lai Mohammed a kwanan nan ya caccaki jam’iyyun adawa a Najeriya, inda ya nemi su daina kuka su rungumi kaddarar rasa nasara a zaben 2023
  • A wani martani ga ministan na yada labarai, jam’iyyar Labour ta ce zaben da aka gudanar na 2023 an yi murdiya a cikinsa
  • Jam’iyyar ta adawa ta kuma zargi hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da kirkirar hanyar rinto a kuri’un da aka kada a zaben na bana

FCT, Abuja - Jam’iyyar Labour ta caccaki Lai Mohammed, ministan yada labarai da al’adu a Najeriya bisa bayanansa na baya-bayan nan kan sakamakon zaben 2023.

Labour ta ce, gwamnatin jam’iyyar APC ta yi duk mai yiwuwa don tabbatar da magudi a zaben da ya gudana a bana.

Bayanan caccakar Lai na zuwa ne ta bakin mukaddashin sakataren yada labarai na Labour na kasa, Obiora Ifor a ranar Lahadi 30 ga watan Afrilu a Abuja, rahoton TheCable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Atiku ne ya lashe zabe: PDP ta caccaki ministan Buhari, ta tono barnar APC

Obi zai kwace mulki a hannun Tinubu, inji LP
Peter Obi na jam'iyyar Labour | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

A cewarsa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Muna kawai bukatar mai girma minista ya sani cewa ta hanyar murdiya a babban zaben 2023, shi kansa, jam’iyyarsa, APC da shugaban jam’iyyar, shugaban kasa Buhari sun kashe baccinsu don haka basu cancanci zaman lafiya ba.”

Zan yi duk abin da zan iya don kwace mulki daga hannun Tinubu, inji Peter Obi

Ta kuma bayyana cewa, makaho ne kadai zai ce ba a yi murdiya a zaben shugaban kasan da ya gabata ba, rahoton Vanguard.

A nasa bangaren, dan takarar shugaban kasa na Labour, Peter Obi ya ce, zan tabbatar da ya kwace hakkinsa na nasara a zaben na bana a kotu.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da ya yi taro da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar Labour a birnin Awka ta jihar Anambra.

A cewarsa, zai bi hanyar doka duk yadda ta kama don tabbatar da ya samu nasara kuma an ba shi kujerar jan ragamar Najeriya.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin Da Aka Yi Wa Wasu Matasa Biyu Yankan Rago a Jihar Filato

PDP ta caccaki APC da minista Lai Mohammed

A wani labarin, kunji yadda jam’iyyar PDP ta bayyana martani ga kalaman da Lai Mohammed ya yi kan yadda zaben bana ya kasance.

PDP ta ce, tabbas Atiku ne ya lashe zabe, kuma APC na son kawo rudu ne ga batun da ke gaban kotu na kalubalantar zaben.

Ya zuwa yanzu, saura kwanaki kasa da 30 a rantsar da Bola Ahmad Tinubu, ana ci gaba da cece-kuce na siyasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel