Gwamnatin Tarayya Za Tayi Wa Ma’aikata Karin Albashi a Afrilu Saboda Cire Tallafin Fetur

Gwamnatin Tarayya Za Tayi Wa Ma’aikata Karin Albashi a Afrilu Saboda Cire Tallafin Fetur

  • An bijirowa gwamnatin tarayya da maganar kara albashin duka ma’aikatan gwamnati da 40%
  • Wani kwamiti ya yi wannan aiki, ya bada shawarar yin hakan a dalilin janye tallafin man fetur
  • Shugabannin kungiyoyin TUC da NLC sun ce maganar ba ta wuce jita-jita ba, aljihunsu bai canza ba

Abuja - Idan dai ba abubuwa sun canza zani ba, ma’aikatan gwamnatin tarayya za su samu karin kudi a albashin da za su karba a karshen watan Afrilu.

Kowane lokaci daga yanzu, Punch ta ce Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai iya amincewa da karin da ake shirin yi wa ma’aikatan tarayyar kasar.

Idan maganar ta samu karbuwa, ma’aikatan gwamnatin za su samu fara cin moriyar wannan kari tun kafin a kai ga janye tallafin man fetur a watan Yuni.

Ma’aikatan gwamnatin tarayya sun shaidawa jaridar cewa za a fito da wasu alawus da karin albashi da za su jawo abin da mutane ke karba ya karu da 40%.

Kara karanta wannan

Kaico: Bashi ya yi mata katutu, ta siyar da jaririyarta mai watanni 18 kacal a wata jiha

Olajide Oshundun ya tabbatar da haka

Da ya zanta da ‘yan jaridar a kebe, Olajide Oshundun wanda shi ne Darektan yada labarai da hulda jama’a na ma’aikatar kwadago, ya yi wannan bayani.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mista Oshundun ya ce watakila daga karshen Afrilun nan, ma’aikata su samu karin albashi.

Osinbajo
Buhari ya yi tafiya ya bar Osinbajo Hoto: @BuhariSallauOnline
Asali: Facebook

Jami’in ya ce ba daga wata mai-ci karin zai soma tasiri ba, daga baya gwamnatin tarayya za ta biya ma’aikata bashin karin Junairu, Fubrairu da Maris.

Amma Oshundun bai bada tabbacin karin zai fara aiki nan-take ba, yake cewa bai da masaniya ko kwamitin da ke aiki ya samu aincewar shugaban kasa.

Albashin ma’aikatan da ke mataki na 1 zuwa 17 zai tashi da 40% a dalilin wannan karin alawus mai dalili da za a fito da shi a dalilin janye tallafin mai.

NLC da TUC sun yi martani

Kara karanta wannan

Gwamna Ortom Na Son Gwamnatin Buhari Ta Dage Yin Wani Kidaya, Ya Bada Dalili

Mataimakin shugaban kungiyar TUC na ‘yan kasuwa, ya ce babu shakka gwamnati na kokarin yin wannan, amma dai maganar ba ta tabbata ba tukuna.

Tommy Etim ya ce zai yi kyau a duba alawus din da ake biyan ma’aikata musamman na kudin mota da gida domin a nan kusan duka albashi suke tafiya.

Da aka zanta da Ma’ajin NLC, Hakeem Ambali ya ce jita-jita kurum ‘yan kwadago suke ji.

Satar kudin fetur

Kwanaki rahoto ya zo cewa wasu ma'aikata sun fallasa cewa Najeriya ta saidawa kasar Sin gangunan fetur miliyan 48, wasu sun sha kwana da kudin.

Ana zargin manyan gwamnati sun karbi miliyoyi a kasar waje. Kwamitin Hon. Mark Tersee Gbillah ya na bincike a Majalisa domin gano gaskiyar lamarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel