Gobara Ta Babbake Wani Sashin Fadar Mai Martaba Ooni na Ife

Gobara Ta Babbake Wani Sashin Fadar Mai Martaba Ooni na Ife

  • An shiga tashin hankali yayin da wutar lantarki ta yi sanadin ƙonewar wani sashi a fadar mai martani Sarkin Yarbawa, Ooni na Ife
  • Mai magana da yawun masarautar ya ce lamarin ya fara ne bayan wani abu daga cikin kayan wuta ya fashe a cikin ginin
  • A cewarsa babu wanda ya rasa rayuwarsa kuma gobarar ba ta shafi kayan al'ada ko guda ɗaya ba

Gobara ta babbake wani sashi a fadar mai martaba Sarkin Ife na jihar Osun wanda ake kira da Ooni na Ife a jihar Osun. Ana zargin gobarar ta tashi ne daga ƙarfin wutar Lantarki.

Daily Trust ta ce wutar ta babbake wani gini a cikin fadar Sarkin da misalin karfe 11:30 na daren ranar Jumu'a 28 ga watan Afrilu, 2023.

Ooni na Ife.
Gobara Ta Babbake Wani Sashin Fadar Mai Martaba Ooni na Ife Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Mazauna yankin sun bayyana cewa wutar ta fara ci rigi-rigi ne bayan wani abu daga cikin kayan wutar lantarki a cikin sashin fadar ya fashe 'Fus' da daren ranar, ya lalata ɓangaren.

Kara karanta wannan

Shugaban Majalisar Dattawa Ya Ja Hankalin Atiku da Obi, Ya Faɗi Abinda Ya Rage Musu Kan Zaben 2023

A cewar wata majiya a yankin Enuwa, Ile-Ife, wurin da fadar Sakin take, lamarin ya faru ne da ƙarfe 11:30 na dare lokacin da hayaƙi ya fara tasowa daga sashin fadar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jami'an hukumar kwana-kwana da masu hidima wa fadar da kuma mazauna yankin ne suka haɗu suka yi nasarar kashe wutar.

Mai magana da yawun fadar Sarkin, Otunba Moses, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ƙara da cewa tuni aka shawo kan lamarin, aka kashe wutar.

Ya ce babu wanda ya rasa rayuwarsa kuma wutar ba ta taɓa ko ɗaya daga cikin kayayyakin al'ada ko ta raunata wani ba, ya ɗora laifin tashin gobarar kan wutar lantarki.

Punch ta rahoto kakakin masarautar na cewa:

"Wani gini da ke cikin fadar Oooni na Ife ya babbake da wuta sanadin wutar lantarki jiya ta misalin ƙarfe 11:30, wani abu daga cikin haɗin wutar lantarki ne ya fashe, daga nan Gobarar ta fara."

Kara karanta wannan

Bayin Allah Da Dama Sun Jikkata, Dukiyoyi Sun Salwanta a Wani Mummunan Fada Da Ya Barke a Jihar Arewa

Hadarin mota ya rutsa da ɗaliban jami'a a Bayelsa

A wani labarin kuma Mummunan Hatsari Ya Rutsa da Daliban Jami'a a Bayelsa, An Rasa Rayuka

Mutum 5 sun mutu yayin da wasu motoci biyu suka yi taho mu gama a kan titi a jihar Bayelsa.

Rahotanni sun nuna cewa ɗaya daga cikin motocin ta ɗauko ɗaliban jami'ar Neja Delta, tana hanyar zuwa Yenagoa, babban birnin jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel