“Ya Sa Ni Kuka”: Matashi Ya Gwangwaje Mahaifiyarsa Da Kyautar Zagayowar Ranar Haihuwa Na Musamman

“Ya Sa Ni Kuka”: Matashi Ya Gwangwaje Mahaifiyarsa Da Kyautar Zagayowar Ranar Haihuwa Na Musamman

  • Wani mai amfani da TikTok ya wallkafa dan gajeren bidiyo da ke nuna lokacin da ya gwangwaje mahaifiyarsa da kyautar zagayowar ranar haihuwa na musamman
  • Bidiyon ya hasko yadda ya kullewa mahaifiyarsa fuska sannan ya tuka ta zuwa filin jirgin sama, inda ya cika ta da mamaki
  • Yanayin mahaifiyar bayan ta amshi kyautar ba zatan ya tsuma zukata, yayin da mutane da dama suka taya su murna

Wata uwa ta samu abun da ta dade tana mafarkin samu a ranar zagayowar ranar haihuwarta lokacin da danta ya shirya mata wata tafiya ta bazata.

Bidiyon da ke nuna lokacin jin dadin na tsakanin uwa da danta ya yadu a dandalin TikTok.

Da ya gwangwaje mahaifiyarsa da abun mamaki
“Ya Sa Ni Kuka”: Matashi Ya Gwangwaje Mahaifiyarsa Da Kyautar Zagayowar Ranar Haihuwa Na MusammanHoto: @kelly_khobbi
Asali: TikTok

A bidiyon wanda @kelly_khobbi- blue ya wallafa, an gano uwar zaune a cikin wata mota yayin danta da sauran mutane da ke motar suka rufe mata fuska.

Kara karanta wannan

Kaico: Matasa a jihar Arewa sun kama tsoho, sun binne shi da ransa bisa zargin maye ne

Bayan sun isa inda za su, wanda ya kasance filin jirgin sama, sai aka jiyo dan nata yana umurtan mahaifiyarsa da ta bude idanunta. Tana aikata hakan, sai ta ga cewa sun isa filin jirgin sama.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Dan nata ya kuma sanar da mahaifiyar tasa cewa sun isa wajen domin tafiya wani waje na daban kuma a cikin jirgi za su yi shawagin da ta dade tana mafarkin yi.

Kalli bidiyon a kasa:

Daga kallon bidiyon mutum zai gane cewa mahaifiyar ta dade tana burin hawa jirgin sama wanda shine kyautar bazata da ta samu daga danta don murnar zagayowar ranar haihuwarta.

Mahaifiyar ta cike da farin ciki sannan ta dungi murmushin jin dadi yayin da take kallon dan nata. Ta so ace wando ta sanya wanda take ganin shine zai fi dacewa da yawo a jirgin sama.

Kara karanta wannan

Tir da talauci: An kirkiri motar da mutum zai iya kiranta a waya, kuma ta zo babu direba

Masu amfani da TikTok sun ji dadin wannan lamari da soyayyar da ke tsakanin dan da uwar tasa sannan sun yi farin ciki da ganin cewa mahaifiyar ta ji dadin abun.

Martanin jama'a

@McBonney ta ce:

"Momi tana burin sanya wando."

@ Nikki Giovanni ta ce:

"Awww yaushe nima zan sanya wannan murmushin a fuskar mahaifiyata wata rana."

@Nessa ta yi martani:

"Ta ce da ka fada mata ta sanya wando da riga."

Bidiyon karamar yarinya tana sallah ya yadu

A wani labari na daban, mun ji cewa wata karamar yarinta ta dauka hankali a soshiyal midiya bayan bayyanar bidiyonta tana sallah kamar wata babba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel