Bayan Shekara 2, Ɗaliban FGC Yauri Guda Hudu Sun Shaki Iskar Yanci

Bayan Shekara 2, Ɗaliban FGC Yauri Guda Hudu Sun Shaki Iskar Yanci

  • Allah ya yi, bayan shafe shekaru biyu a tsare, huɗu daga cikin ɗaliban FGC Yauri 11 da ke hannun yan bindiga sun kubuta
  • Ɗaliban sun shaƙi yanci daga hannun ƙasurgumin ɗan bindigan nan, Dogo Giɗe, bayan shafe dogon lokaci ana tattauna wa
  • Tun a shekarar 2021 yan bindiga suka sace ɗaliban FGC Birnin Yauri da malamai a wani farmaki da suka kai makarantar

Kebbi - Ɗaliban makarantar kwalejin gwamnatin tarayya (FGC) da ke birnin Yauri a jihar Kebbi huɗu daga cikin 11 da suka rage hannun yan bindiga, sun shaki iskar yanci.

Jaridar Daily Trust ta ce ɗaliban mata huɗu sun kubuta ne shekara biyu bayan yan bindigan sun yi awon gaba da su daga makaranta a jihar Kebbi.

FGC Yauri
Bayan Shekara 2, Ɗaliban FGC Yauri Guda Hudu Sun Shaki Iskar Yanci Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Ɗaliban guda huɗu, Bilha Musa, Faiza Ahmed, Rahma Abdullahi da kuma Hafsa Murtala, sun kubuta daga hannun ƙasurgumin ɗan bindiga, Dogo Gide, ranar Jummu'a da yamma.

Kara karanta wannan

A Masallacin Idi, Sarkin Musulmi Ya Yi Magana Mai Jan Hankali Kan Atiku da Wasu Mutane a Najeriya

Salim Kaoje, ya shaida wa jaridar cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Sai da aka kwashe kwanaki 6 ana tattaunawa a cikin Daji kafin a samu nasarar kubutar da ɗaliban mata guda huɗu."
"Har yanzu muna da ragowar ɗalibai Bakwai da suke tsare hannunsu kuma iyayen biyu daga cikinsu na can cikin jejin suna kokarin kubutar da su."

Shin an biya kuɗin fansa?

Kaoje ya kara da cewa sai da iyayen suka biya kuɗin fansa wanda ba'a san adadin yawansu ba gabanin kubutar da yaran. Sun sayar da kadarorinsu kuma wasu yan Najeriya sun tallafa musu.

A watan Janairu, Salim Kaoje, ya tabbatar da cewa sun fara tattaunawa da Dogo Gide bayan sun nemi mahaifiyarsa ta shige musu gaba, kamar yadda Ripples ta rahoto.

A ranar 17 ga watan Yuni, 2021, 'yan bindiga suka farmaki FGC Birnin Yauri, inda suka yi awon gaba da gwamman ɗalibai da malamai a makarantar mai ƙunshe da maza da mata.

Kara karanta wannan

Asiri Ya Tonu: An Kama Wasu Muggan Mutane Sama da 20 Ɗauke da Makamai Ana Dab da Sallah a Arewa

Mahara Sun Kashe Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Kasa a Mali

A wani labarin kuma Mahara Sun Halaka Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Ƙasa da Wasu Manyan Jami'ai 4

Wani harin kwantan bauna ya yi ajalin manyan kusoshin gwamnati ƙasar Mali har su 5, an nemi direbansu an rasa har kawo yanzu.

Daga cikin waɗanda aka kashe har da shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa a babban birnin ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel