Rai Bakon Duniya: Mahaifiyar Tsohon Gwamnan Jihar Imo, Emeka Ihedioha, Ta kwanta Dama

Rai Bakon Duniya: Mahaifiyar Tsohon Gwamnan Jihar Imo, Emeka Ihedioha, Ta kwanta Dama

  • Tsohon gwamnan jihar Imo, Emeka Ihedioha, ya yi babban rashi na mahaifiyar sa, Dame Dorothy Nsonma Ihedioha
  • Dame Dorothy, wacce ta yi murnar cika shekara 90 a duniya a ranar 28 ga watan Agustan 2022, ta mutu ne a birnin tarayya Abuja, a ranar Alhamis 20 ga watan Afirilu 2023
  • Iyalan marigayiyar sun ƙara da cewa za a sanar da lokacin kai ta makwancin ta na gaskiya nan gaba kaɗan inda suka nemi a taya ta da addu'o'i

Abuja - Mahaifiyar Emeka Ihedioha, tsohon gwamnan jihar Imo, ta kwanta dama. Dame Dorothy Nsonma Ihedioha ta mutu ne tana da shekara 90 a duniya.

A cewar wata sanarwa da tsohon gwamnan ya sanya a shafin sa na Facebook, marigayiyar ta bar duniya ne a ranar Alhamis, 20 ga watan Afirilun 2023 a birnin tarayya Abuja, a kusa da iyalanta.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: An Rasa Rayuka Yayin da Wani Gini Ya Tumurmushe Mutane a Abuja Cikin Azumi

Mahaifiyar Emeka Ihedioha ta riga mu gidan gaskiya
Dame Dorathy Ihedioha, ta riga mu gidan gaskiya Hoto: Emeka Ihedioha
Asali: Facebook

Dame Dorathy ta mutu ta bar duniya inda ta bar ƴaƴa, jikoki da ƴaƴan jikoki.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Mama ta yi bikin cikar ta shekara 90 a duniya a ranar 28 ga watan Agustan 2022.
A yayin da mu ke nuna godiyar mu ga abokai da masu mana fatan alkhairi waɗanda suka kasance tare da mu, musamman a lokacin da mahaifiyar mu ke kan gargara, muna roƙon ku da ku tuna da mu a cikin a addu'o'in ku."

Ihedioha ya kuma ƙara da cewa za a sanar da lokacin sada ta da gidan ta na gaskiya nan ba da jimawa ba.

Allah Ya Yiwa Shahrarren Dan Kwangila a Jihar Kano, Alhaji Sani Dahiru Yakasai, Rasuwa

A wani rahoton na daban kuma, kun ji yadda Allah maɗaukakin sarki ya karɓi ran wani shahararren ɗan kwangila a jihar Kano, da ke yankin Arewa maso Gabas na tarayyar Najeriya.

Kara karanta wannan

Kaico: Bashi ya yi mata katutu, ta siyar da jaririyarta mai watanni 18 kacal a wata jiha

Alhaji Sani Dahitu Yakasai wanda shine shugaban wani kamfanin da ke yin gine-gine, ya koma ga mahaliccin sa ne bayan ya yi fama da doguwar jinya. Marigayin ya rasu ya bar mata, ƴaƴa da jikoki.

Tuni aka yi jana'izar mamacin sannan aka kai shi makwancin sa na gaskiya kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

Asali: Legit.ng

Online view pixel