Karshen Ramadana 2023: Bayanin Ganin Jinjirin Watan Shawwal Na Karamar Sallah a Najeriya

Karshen Ramadana 2023: Bayanin Ganin Jinjirin Watan Shawwal Na Karamar Sallah a Najeriya

  • Ya zuwa yanzu, kwamitin duban wata a Najeriya ya ce ba a wata ba a wasu bangarori daban-daban na Najeriya
  • A yau ne al'ummar Musulmi suka kai azumi na 29 a watan Ramadana mai alfarma, inda ake sa ran ganin wata a yau
  • Tuni a kasar Saudiyya, an ga watan Ramadana, gobe Juma'a za a yi karamar sallah a kasar ta Larabawa

Najeriya - Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da zuba ido don jin labarin ganin jinjirin watan Shawwal a garuruwa da yankuna daban-daban na Najeriya.

A wata gajeruwar sanarwar da kwamitin duban wata ya fitar da yammacin yau Alhamis, ba a jinjirin watan ba a jihohi sama da biyar na Najeriya.

Sai dai, kwamitin ya ce yana ci gaba da zuba ido da sauraran rahotanni daga sauran jihohi da garuruwa a kasar.

Kara karanta wannan

Eid-Al-Fitr: An Ga Jinjirin Watan Karamar Sallah Shawwal 1444/2023 a Saudiyya

Sarkin Musulmi ya tabbatar da ganin wata
Sarkin Musulmi na Najeriya | Hoto: dailypost.ng
Asali: Facebook

A cewar wani yankin sanarwar:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ya zuwa yanzu rahotannin da ake samu daga Bauchi, Nafada (jihar Gombe), Maiduguri, Abuja, Dengi (jihar Filato), Odeomu (jihar Osun) duk ba a ga wata ba."

Legit.ng Hausa ta gano cewa, ba a ga wata ba a Najeriya, muna nan muna jiran sanarwa daga ofishin sarkin Musulmi ko akwai labari.

Sarkin Musulmi zai yi bayani

A halin da ake ciki, sarkin Musulmi ya sanar da cewa, a ranar Juma;a ne za a yi sallah karama a Najeriya.

Ya bayyana hakan ne bayan dogon lokacin da Musulman Najeriya suka jira don jin ta bakinsa, kamar yadda wani sako ya nuna.

Wannan na nufin cewa, gobe Juma'a za ta kasance 1 ga watan Shawwal, wanda za ta yi daidai da 21 ga watan Afrilun miladiyyan Annabi Isa.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: An Rasa Rayuka Yayin da Wani Gini Ya Tumurmushe Mutane a Abuja Cikin Azumi

An ga watan Shawwal a Saudiyya

A wani labarin kuma, kunji yadda rahotanni daga kasar Saudiyya ke bayyanawa da tabbatar da ganin jinjirin watan Shawwal a wannan shekarar.

Hakan na zuwa ne daidai lokacin da Musulmai suka kammala azumi na 29 a cikin watan Ramadana mai alfarma na bana.

A baya, rahotanni daga masana masu bincike kna hasashen yanayi da taurari sun ce ba lallai a ga watan Shawwal a ranar 20 ga watan Afrilu ba saboda wasu dalilai na yanayi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel