Jerin Gwamnoni 8 da Ka Iya Tashi da Kujerun Minista a Mulki Bola Ahmad Tinubu

Jerin Gwamnoni 8 da Ka Iya Tashi da Kujerun Minista a Mulki Bola Ahmad Tinubu

Gabanin rantsar da Bola Ahmad Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu, rahoton jaridar Leadership ya bayyana wasu gwamnonin APC masu bari gado da ka iya zama makusantan mulkin Tinubu.

A kasa, mun tattaro muku jerin gwamnonin APC da ke shirin barin gadi da kuma yiwuwar samun mukami a mulki Tinubu.

Masu iya zama ministoci a mulkin Tinubu
Wasu gwamnonin Najeriya da kuma Tinubu | Hoto: Bola Tinubu, Abdullahi Ganduje, Bello Matawalle, Atiku Bagudu, Simon Lalong
Asali: Facebook

1. Bello Matawalle

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya rasa kujerarsa a kokarin da ya yi na komawa mulki, inda Dauda Lawal na PDP ya lashe zaben gwamnan jihar.

Rahoton ya bayyana cewa, akwai yiwuwar Matawalle ya kasance cikin na hannun daman Tinubu a jerin ministocinsa kasancewar ya rasa kujerarsa ta gwamna.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

2. Simon Lalong

Ba kamar gwamna Matawalle ba, Simon Lalong na Filato zai kasara mulkinsa a wa’adi na biyu a watan Mayun bana.

Sai dai, ya gaza samun damar nada gwamnan da yake so, kana dan takarar PDP na sanata a mazabarsa, Napoleon Bali ne ya lashe zaben sanatan da Lalong ya nema.

Ganin cewa ya shine daraktan kamfen Tinubu/Shettima a bana, zai iya zama minista idan aka rantsar da Tinubu a Mayu.

3. Abubakar Bagudu

Gwamnan Kebbi Bagudu shi ma na kan gargarar karasa wa’adinsa na biyu a mulki. Sai dai, kamar dai Lalog, bai samu damar zama sanata ba a zaben bana, inda tsohon gwamnan jihar Adamu Aliero ya lashe zaben mazabarsa.

A baya-bayan nan Bola Tinubu ya nada kwamitin karbar mulki, don haka ake ganin akwai yiwuwar gwamnan na Kebbi ya zama cikin jerin sanatocin Tinubu.

4. Mohammed Badaru Abubakar

Gwamna Badaru na Jigawa zai mika mulki nan ba da jimawa ga zababben gwamnan jihar, umar Namadi bayan kammala wa’adi biyu na mulki.

Yana daya daga cikin gwamnonin Arewa da suka tsaya tsayin daka wajen tabbatar da Tinubu ya yi nasara a zaben bana na 2023.

Hakan ka iya zame masa damar zama daya daga na gaban goshin mulkin Tinubu a wnanan karon.

5. Nasir El-Rufai

Duk da cewa El-Rufai ya nuna rashin kaunarsa ga wata kujera bayan mika mulki ga Uba Sani a watan Mayun bana, akwai yiwuwar Tinubu ya jawo shi jika.

A cewar rahoton na Leadership, wani mai nazarin siyasar gwamnan da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, an ambaci El-Rufai cikin wadanda za su yi aiki a mulkin Tinubu.

6. Ben Ayade

Gwamna Ben Ayade na Cross River ya rasa zaben sanata da aka yi a ranar 25 ga watan Faburairun bana.

Akwai yiwuwar gwamnatin Tinubu ta yi masa gata ta hanyar ba shi kujerar minista nan ba da jimawa ba.

7. Abdullahi Ganduje

Gwamna Ganduje na Kano ba kawai na kusa da Tinubu bane, ya yi kokari wajen tabbatar da dan takarar na APC ya zama shugaban kasan Najeriya.

Tunda Ganduje bai nemi sanata ba a Kano, akwai yiwuwar Tinubu ya yi masa gata ta hanyar ba shi minista a nan gaba

8. Kayode Fayemi

Gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi ka iya zama cikin wadanda Tinubu zai gwangwaje da kujerar minista a bana.

Ya kasance na hannun daman zababben shugaban kasa, kuma yana daya daga wadanda suka janyewa Tinubu a zaben fidda gwanin APC na bara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel