Matashi Ya Kashe Sama Da Miliyan N160 Wajen Siyan Motar Alfarma, Bidiyon Ya Ja Hankali

Matashi Ya Kashe Sama Da Miliyan N160 Wajen Siyan Motar Alfarma, Bidiyon Ya Ja Hankali

  • Wani matashi da ya kashe miliyoyin naira wajen siyan motar Rolls Royce Cullinan ya baje kolin ta a wani bidiyo da ya yadu
  • Mutumin ya isa ga tsadaddiyar motar alfarma sannan ya bude kofarta don mutane su ga kyan cikinta
  • Mutane da dama sun taya shi murna da nuna sha’awarsu ga motar yayin da wasu ke son sanin aikin da yake yi

Wani matashi, @ahumadake123, ya je dandalin TikTok don baje kolin motarsa kirar Rolls Royce Cullinan a wani bidiyo da ya yadu. Ya dauki lokacin da ya shiga motar.

An ajiye motar a harabar wani gida. Bayan ya zauna kan kujerar direba, sai matashin ya yi nuni ga yatsa don baje kolinta.

Matashi cikin wata tsadaddiyar mota
Matashi Ya Kashe Sama Da Miliyan N160 Wajen Siyan Motar Alfarma, Bidiyon Ya Ja Hankali Hoto: @ahumadake123
Asali: TikTok

Matashi da motarsa kirar Rolls Royce Cullinan

Kujerun motar jajjaye ne. Komai na cikin motar Kamar yadda ake sa ran gani daga Rolls Royce ya kasance hadadde.

Kara karanta wannan

"Dan Allah Ka Mana Alfarma Ɗaya Tak" Tsohon Minista a Najeriya Ya Aike da Sako Ga Peter Obi

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewar CarBuzz, farashin motar yana tsakanin .

Motar ta burge mutane da dama da suka garzaya sharhi na mutumin.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama’a sun yi martani

Vanity ya ce:

“Ka gwangwaje yaronka.”

2G Glory ta ce:

“Allah ya albarkace ka dan’uwa.”

bennyfunds ya ce:

“Allah ya yi mun irin taka.”

Franklin ya ce:

“Kana bukatar mai kula da mota ko mutumin da zai dunga wanke maka.”

chibuikesakuel933 ya ce:

“Rolls ce faah.”

Nzube ya tambaya:

“Aikin me kake yi dan uwa?”

Matashi ya tallafawa wani tsoho mai tura baro, bidiyon ya tsuma zukata

A wani labari na daban, wani matashi ya sha ruwan yabo a soshiyal midiya bayan ya gwangwaje wani tsoho da bai sani ba da sha tara ta arziki.

Mutumin na a kan hanyar tafiya kawai sai ya ci karo da wannan tsohon yana tuka baro yayin da yake kwasan bola daga wurare daban-daban.

Kara karanta wannan

An Samu Wanda Ya Fito Takarar Shugaban Majalisa, Ya Ziyarci Gwamnoni 24 a Boye

Tausayin tsohon ya darsu a ransa inda ya dauke shi zuwa wani shagon siyar da kayayyaki ya siya masa tufafi da takalma da kuma kayan masarufi da suka hada da shinkafa da man gyada.

Bayan ya gama masa wannan abubuwan alkhairin, sai ya kuma saka shi a cikin motarsa inda ya dauke shi zuwa gidansa tare da siyayyan da ya yi masa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel