Mutane Da Dama Sun Mutu Yayin da Fada Ya Kaure Tsakanin Hausawa Da Fulani a Sokoto

Mutane Da Dama Sun Mutu Yayin da Fada Ya Kaure Tsakanin Hausawa Da Fulani a Sokoto

  • An yi mummunan karo tsakanin Hausawa da Fulani a yankin Gwadabawa da ke jihar Sokoto
  • Jama'ar yankin Gwadabawa sun shiga tashin hankali saboda rikicin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane masu yawan gaske
  • Yanzu haka ana zaman dar-dar a yankin saboda fargabar kawo hare-haren ramuwar gayya daga bangaren Fulani

Sokoto - Jaridar Vanguard ta rahoto cewa an samu tashin hankali a garin Gwadabawa da ke jihar Sokoto, bayan wani rikici ya kaure tsakanin Fulani da Hausawa a yankin.

Mummunan karon ya yi sanadiyar mutuwar mazauna yankin da dama daga bangarorin biyu, ciki harda jami'an tsaro.

Taswirar jihar Sokoto da ke arewa maso yamma
Mutane Da Dama Sun Mutu Yayin da Fada Ya Kaure Tsakanin Hausawa Da Fulani a Sokoto Hoto: Punch
Asali: UGC

Wani jami'in yankin, Aminu Gwadabawa, ya fadama VOA Hausa a wata hira da ta yi da shi a ranar Asabar cewa mutane na zaman dar-dar a yankin, yayin da rikicin ya yi sanadiyar mutuwar wani soja.

Kara karanta wannan

A Cikin Ramadan Yan Bindiga Sun Tare Hanyar Kaduna Zuwa Abuja Sun Sace Matafiya

Aminu ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Suna tsoron hare-haren ramuwar gayya daga yan bindigar Fulani."

Wadanda suka tsallake rijiya da baya a harin sun magantu

A cewar wani da ya tsallake rijiya da baya:

"Fulani sun farmaki dan uwana da wukake. Amma yana da wani kafiya da ba zai tar abu mai tsini ya shiga jikinsa ba.
"Don haka sai suka ci gaba da kai masa hari sannan suka yi nasarar fille kansa daga jikinsa."

Hakazalika, wani Bafulatani da ya tsira daga rikicin ya ba da nashi labarin.

A cewarsa:

"Sau biyu aka harbe ni amma na tsira. Na roke su da kada su kashe ni. Amma sai suka harbe ni."

Rundunar yan sanda ta yi martani

VOA Hausa ta rahoto cewa da aka tuntubi yan sandan jihar Sokoto, sun ce har yanzu suna jiran cikakken bayani kan harin.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: A Watan Azumi, 'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wani Sarki Mai Martaba a Arewa

An tattaro cewa an kashe mutane da dama yayin rikicin inda wasu da dama suka jikkata.

Rahoton ya kuma nuna cewa ana yawan samun hare-haren yan bindiga a baya-bayan nan a yankin don haka bai zama sabon abu ba.

An rahoto cewa yan bindiga sun farmaki garuruwa a yankin Rabah da sauran wurare a jihar da ke arewa maso yamma.

Matasa sun zane basarake a jihar Taraba, sun kona fadarsa

A wani labari na daban, mun ji cewa fusatattun matasa sun zane basarake mai daraja ta uku a jihar Taraba, Kwe Ando Madugu, saboda zarginsa da baiwa makiyaya da ke kashe-kashe a yankinsu mafaka

Asali: Legit.ng

Online view pixel