Yadda Matasa Suka Zane Wani Basaraken Taraba, Sun Kona Fadarsa

Yadda Matasa Suka Zane Wani Basaraken Taraba, Sun Kona Fadarsa

  • Wasu matasa sun yi wa basaraken Taraba mai daraja ta uku, Kwe Ando Madugu mugun duka tare da kona fada da ababen hawarsa
  • Fusatattun matasan sun yi wa fadar Madugu da ke karamar hukumar Ussa tsinke, inda suka hau shi da duka har ta kai sun ji masa rauni
  • Suna zargin basaraken da hada baki da makiyaya da ke yankin wadanda ake zargi da aikata kashe-kashe da sace-sacen mutane
  • Rundunar yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar mummunan al'amarin inda ta ce ta kaddamar da bincike a kai

Taraba - Wani basarake mai daraja ta uku a jihar Taraba, Kwe Ando Madugu, ya tsallake rijiya da baya a karamar hukumar Ussa bayan wasu matasa sun farmake shi tare da kona fadarsa da motoci.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa matasan sun yi wa basaraken dukan kawo wuka sannan suka ji masa rauni yayin da suka cinna wuta a fadarsa.

Kara karanta wannan

Abin takaici: An kashe malamin addinin Muslunci daidai lokacin buda baki a wata jiha

Jami'an yan sanda rike da bindigogi
Yadda Matasa Suka Zane Wani Basaraken Taraba, Sun Kona Fadarsa Hoto: Premium Times
Asali: UGC

An tattaro cewa matasan sun farmaki fadar Kwe Ando Madugu a ranar Litinin bayan ya ki bin umurninsu na neman a fatattaki makiyaya da zaune a yankin.

Suna dai zargin makiyayan da kasancewa da hannu a kashe-kashe da kuma garkuwa da mutane a wannan yanki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Matasan sun zargi basaraken da hada kai da makiyayan. Kuma a yanzu haka yana kwance a asibiti an ba shi gado.

Rundunar yan sanda ta yi martani

Kakakin rundunar yan sandan jihar Taraba, SP Usman Abdullahi, wanda ya tabbatar da farmakin da aka kai wa basaraken ya ce ana gudanar da bincike a yanzu haka, rahoton Aminiya.

Yan bindiga sun yi garkuwa da matar basaraken Kano da dansa

A wani labarin kuma, mun ji cewa wasu yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace matar hakimin kauyen Nasarawa da ke karamar hukumar Tsanyawa ta jihar Kano.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kame tsagerun 'yan bindiga 2 da suka addabi jihohin Arewa

Maharan dai sun farmaki gidan basaraken ne da tsakar dare sannan suka tisa keyar matarsa, Halima da kuma dansa Dahiru zuwa wani wuri da ba a sani ba.

Rundunar yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar al'amarin inda ta ce tuni ta tura wata tawagar ceto a kokarinta na ceto mutanen ba tare da sun illata ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel