“Na Shiga Rudu”: Jama’a Sun Yi Cece-Kuce Kan Bidiyon Sauyawar Wasu Sabbin Ma’aurata

“Na Shiga Rudu”: Jama’a Sun Yi Cece-Kuce Kan Bidiyon Sauyawar Wasu Sabbin Ma’aurata

  • Wani bidiyo da ya yadu na wasu ma'aurata ya girgiza intanet saboda yadda suka fara har zuwa inda abun ya kai su
  • Kamar yadda bidiyon ya nuna, ma'auratan sun san junansu tun amaryar na yar kankanuwar yarinya
  • Bidiyon na dauke da tsohon hoto na wani yaro dauke da wata yar karamar yarinya kuma karshen ya nuno aurensu

Kaddara na da yadda take hada kowani mutum da abokin rayuwarsa koda kuwa ta yanayi da ba'a taba zato ba.

Yayin da wasu mutane ke nasarar haduwa da abokan rayuwarsu tun suna kananan yara, wasu kan yi zaman jira na dogon lokaci kafin su hadu.

Hoton Amarya da ango na baya da yanzu
“Na Shiga Rudu”: Jama’a Sun Yi Cece-Kuce Kan Bidiyon Sauyawar Wasu Sabbin Ma’aurata Hoto: @iamtiwabae
Asali: TikTok

Wata matashiya yar Najeriya ta girgiza intanet bayan ta bayyana yadda ta hadu da mijinta tun tana yar karamar yarinya.

Wani bidiyo da ta wallafa a shafinta na TikTok, @iamtiwabae, ya nuno wani tsohon hotonsu tun na shekarun baya.

Kara karanta wannan

"Kan 300k": Yadda Uba Ya Gwada 'Yarsa Don Ya Gane Ko Tana Taba Sana'ar Karuwanci a Makaranta

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A bidiyon, mutumin ya dauki matashiyar wacce take yar mitsitsiyan yarinya a lokacin. A wani yanayi mai nuna kaddara, sun yi aure bayan shekaru 24.

Bidiyon ya nuna yadda aka yi didiman bikinsu ciki harda hotunansu sanye da kayan amarya da ango.

Jama'a sun yi martani

@Gold ta yi martani:

"Wanene kuma ya yi gaggawan tura bidiyon??? Ina da saurin fushi dan Allah."

@aaaaSMum ta ce:

"Wato kenan matarka ka dauka haka, lallai Allah kadai ne mai yi."

@adaobionyebuchi ta ce:

"Daga zaman raino zuwa mijin yarinya."

@Akwe Favour ta yi martani:

"Ina tayaku murna."

@Christabel Ann ta rubuta:

"Na shiga rudani."

@mimi ta yi martani:

"Tsaya ban fahimta ba faaa."

@Juliet Sylvester ta yi martani:

"Allah dai ya kyauta..ina gayen nan da ya rike ni ina yar karama?"

@user9722438165070 ya yi martani:

Kara karanta wannan

“Na Ga Ta Kaina”: Uwa Ta Wallafa Bidiyon Yadda Diyarta Ta Hada Mata Waje, Ta Shige Durowa Ta Yi Zamanta

"Na zata mahaifinta ne kai."

@Trishgirl ta yi martani:

"Ban gane abun ba? Na ma zata kanwarsa ce."

Uba ya gwada diyarsa don gano ko tana sharholiya a makaranta

A wani labarin kuma, wani uba dan Najeriya wanda ke son tabbatar da irin rayuwar da diyarsa ke yi a makaranta ya shirya mata gadar zare, ya dauko hayar wata da ta yi mata tayin kwana da wani namiji kan 300k.

Sai dai diyar tasa bata basa kunya ba domin dai ta ki amsa tayin inda ta jaddada cewar ita bata taba sanin wani da namiji ba a tayuwarta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel