A Gano Jirgin da Ya Dauko Mai Dauke da Cutar Ebola daga Kasar Waje Ya Shigo da Ita Najeriya

A Gano Jirgin da Ya Dauko Mai Dauke da Cutar Ebola daga Kasar Waje Ya Shigo da Ita Najeriya

  • Sababbin bayanai sun nuna cewa matar da aka tabbatar tana ɗauke da cutar Ebola a Abuja ta shigo Najeriya ne a ranar 3 ga Oktoba, 2026
  • Gwamnatin Uganda ta buƙaci Najeriya ta samar da cikakkun bayanan tafiyar matar da na lafiyarta, tana mai cewa ba ta kamu da cutar a ƙasarta ba
  • An gano mutane 44 da suka yi mu'amala da matar, yayin da gwamnatin tarayya ta sanya cibiyoyin lafiya da asibitocin matafiya a kan shirin ko-ta-kwana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Sababbin bayanai sun bayyana game da matar da aka tabbatar tana ɗauke da cutar Ebola a Babban Birnin Tarayya (FCT), Abuja.

Bayanai sun tabbatar da cewa an gano cewa ta shigo Najeriya ne ta jirgin saman Ethiopian Airlines a farkon wannan wata na Oktoba da muke ciki.

Kara karanta wannan

Ebola: Atiku ya gano matsala a shirin Tinubu, ya nemi bahasi kan N10bn da aka ware

Ethiopian Airlines.
Jirgin kamfanin sufuri na Ethiopian Airlines bayan ya sauka a filin jiragen sama Hoto: Ethiopian Airlines
Source: Facebook

Lokacin da matar ta shigo Najeriya

Wata babbar jami’ar harkokin sufurin jiragen sama, wadda ta nemi a sakaya sunanta saboda ba ta da izinin yi wa manema labarai bayani kan lamarin, ta tabbatar da hakan ga jaridar Vanguard.

Ma'aikaciyar ta shaida cewa matar da ke dauke da cutar Ebola ta shigo Najeriya ne a ranar 3 ga Oktoba, 2026.

Uganda ta nemi karin bayani

Wannan na zuwa ne yayin da gwamnatin Uganda ta buƙaci Najeriya ta ba ta cikakkun bayanan tafiyar matar da bayanan kula da lafiyarta.

Uganda ta dage cewa matar ba ta kamu da cutar a kasarta ba, domin a cewarta babu wanda ya kamu da Ebola a ƙasar.

A cewar jami’ar, matar da ke dauke da Ebola ta sauka a filin jirgin saman ƙasa da ƙasa na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja ne a jirgin Ethiopian Airlines mai lamba ET333.

Matakin da Najeriya ta dauka

Kara karanta wannan

Ebola: Gwamnatin Tinubu ta fayyace gaskiya ga 'yan Najeriya

Wannan bayani zai taimaka wajen gano mutanen da suka yi hulɗa da ita, bayan da Ministan Lafiya, Farfesa Muhammad Pate, ya tabbatar da bullar cutar a babban birnin ƙasar.

A baya, Pate ya bayyana cewa matar ta dawo Najeriya daga Uganda ta jirgin sama na ƙasa da ƙasa, sannan ta shafe kwanaki da dama tana samun kulawar likitoci a wani asibitin kudi a Abuja kafin a tabbatar da cewa tana ɗauke da cutar.

Tun daga lokacin, an mayar da ita wata cibiyar killace majiyyata da aka keɓe domin kula da masu irin wannan cuta, inda take karɓar magani a halin yanzu.

Ebola.
Cutar Ebola a dakin gwaje-gwaje ana aiki a kanta Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

An gano waɗanda suka yi hulɗa da ita

Bayan tabbatar da cutar, an fara wani babban aikin haɗin gwiwa da ya haɗa da Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya, Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya (NCDC) da Sashen Kula da Lafiya da Muhalli na Abuja.

Hukumomin kula da lafiyar jama’a sun gano mutane 44 da suka yi hulfa da matar zuwa yanzu. Mutanen sun haɗa da ma’aikatan lafiya, sauran majiyyatan da ke asibitin, masu kula da ita da kuma mutanen da ke da alaƙa da hanyoyin tafiyarta.

Kara karanta wannan

Dan takarar shugaban kasa ya nemi aron Aso Rock domin kaddamar da kamfen

Abubuwa 10 game da cutar Ebola

Kun ji cewa gwamnatin Najeriya ta tabbatar da bullar cytar Ebola bayan yi wa wata mata da ta dawo Najeriya daga kasar waje gwaji a Abuja.

Ebola cuta ce mai tsanani da ke yaɗuwa, kuma tana iya haddasa mutuwa idan ba a gaggauta ba da kulawar lafiya ba. Mun tattaro muku abubuwa 10 game da wannan cuta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262