Ebola: Atiku Ya Gano Matsala a Shirin Tinubu, Ya Nemi Bahasi kan N10bn da Aka Ware
- Atiku Abubakar ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya yi bayani kan yadda aka kashe Naira biliyan 10 da aka ware kan cutar Ebola
- Tsohon mataimakin shugaban kasar ya nuna damuwa kan jinkirin sanar da bullar cutar a Abuja, inda aka gano mu'amala da mutane 44
- Atiku ya bukaci gwamnati ta bayyana kudaden da aka saki, kwangilolin da aka bayar da kayan da aka samar kan lamarin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya caccaki Bola Tinubu kan ware makudan kudi saboda tunkarar cutar Ebola.
Atiku ya bukaci Tinubu ya yi bayani kan Naira biliyan 10 da aka amince a ware domin shirin tunkarar cutar Ebola a watan Yuni.

Source: Twitter
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC ya gabatar da bukatar ne a cikin wata sanarwa da Phrank Shaibu, daraktan sadarwa da dabarun yakin neman zabensa, cewar TheCable.
Sake bullar cutar Ebola a Abuja
Kalaman Atiku sun biyo bayan sanarwar da Ali Pate, ministan lafiya mai kula da harkokin lafiya da walwalar jama’a, ya yi cewa gwamnatin tarayya ta tabbatar da bullar cutar Ebola a Abuja, tare da gano mutane 44 da suka yi mu’amala ta kusa da mara lafiyar domin bibiyarsu da hana yaduwar cutar.
Atiku ya ce tabbatar da bullar cutar Ebola a Abuja ya haifar da tambayoyi kan shirin gwamnati na tunkarar cutar da yadda take daukar matakan dakile ta.
Ya ce:
“Ebola babbar barazana ce ga lafiyar jama’a. ’Yan Najeriya sun cancanci daukar matakin gaggawa, shugabanci nagari da kuma sanin gaskiya.
"Sai dai bullar cutar ta farko da aka tabbatar a Abuja ta fallasa tambayoyin da har yanzu ba a amsa ba kan shirin tunkarar cutar, sa ido da kuma kare ma’aikatan lafiya. Dole ne Tinubu ya yi bayani kan Naira biliyan 10 da ya ce za a saki nan take a watan Yuni.”

Source: Getty Images
Bukatar Atiku ga gwamnatin Tinubu
Atiku ya bukaci shugaban kasar ya bayyana adadin kudaden da aka saki, ranakun biyan kudaden, cikakkun bayanan kwangilolin da aka bayar, wadanda suka amfana da su da kuma kayayyakin da aka samar.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce Tinubu dole ne ya yi bayani idan har ba a saki kudaden ba.
Ya ce:
“Tinubu dole ne ya bayyana dalilin da ya sa ya sanar da bayar da kudin gaggawa, amma kudin bai isa ga mutanen da ke da alhakin kare ’yan Najeriya ba. Sanarwar manema labarai ba za ta maye gurbin binciken kudade ba.”
Atiku ya kuma nuna shakku kan lokacin da aka samu rahoton bullar cutar, inda ya ce mara lafiyar ya shigo Najeriya ranar 5 ga Oktoba, ya fara nuna alamun cutar ranar 7 ga Oktoba, sannan ya nemi magani a wani asibiti mai zaman kansa ranar 11 ga Oktoba.
Ya ce gwamnati ba ta sanar da jama’a bullar cutar Ebola a hukumance ba sai ranar 20 ga Oktoba, kwanaki tara bayan mara lafiyar ya nemi magani.

Kara karanta wannan
A gano jirgin da ya ɗauko mai ɗauke da cutar Ebola daga ƙasar waje ya shigo da ita Najeriya
Atiku ya yi zargin cewa ba a sa ido kan mutane 44 da suka yi mu’amala ta kusa da mara lafiyar a wannan lokacin ba, sannan ma’aikatan lafiya na asibiti mai zaman kansa da suka kula da shi ba su da isassun kayan kariya.
An gano jirgin da ya dauko mata mai Ebola
A wani labarin, an ji cewa sababbin bayanai sun nuna cewa matar da aka tabbatar tana ɗauke da cutar Ebola a Abuja ta shigo Najeriya ne a ranar 3 ga Oktoba, 2026.
Gwamnatin Uganda ta buƙaci Najeriya ta samar da cikakkun bayanan tafiyar matar da na lafiyarta, tana mai cewa ba ta kamu da cutar a ƙasarta ba.
An gano mutane 44 da suka yi mu'amala da matar, yayin da gwamnatin tarayya ta sanya cibiyoyin lafiya da asibitocin matafiya a kan shirin ko-ta-kwana.
Asali: Legit.ng

