CDC Afirka: Abin da Ya Sa Babu Maganin Nau'in Cutar Ebola da Ta Bulla a Najeriya
- Shugaban hukumar CDC ta nahiyar Afirka ya yi magana kan rashin samar da magani/rigakafin nau'ik cutar Ebola da ta shiga Najeriya
- Wani kamfanin Afirka da ke Masar na gudanar da gwaje-gwajen rigakafin cutar Ebola ta nau’in Bundibugyo
- Najeriya ta tabbatar da mutum na farko da ya kamu da Ebola nau’in Bundibugyo daga wata ƙasa a ranar 20 ga Oktoba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Shugaban hukumar Kula da Cututtuka ta Afirka (Africa CDC), Dakta Jean Kaseya, ya dora laifin rashin samar da rigakafin Ebola a Afirka kan kasashen duniya.
Ya ce nuna halin ko in kula na kasashen duniya ne ya sa har yau babu rigakafin da aka amince da shi kan nau’in cutar Ebola ta Bundibugyo.

Source: Facebook
Kaseya ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin wata hira da shirin The Morning Brief na gidan talabijin na Channels Television, inda ya yi kira ga ƙasashen Afirka da su ƙara saka kuɗi a binciken rigakafi da samar da shi.

Kara karanta wannan
Majalisar ɗinkin duniya ta yi magana kan nau'in Cutar Ebola da ya ɓulla a Najeriya
Dalilin rashin samae da maganin Ebola
Ya kuma bayyana acewa da a ce cutar ta shafi ƙasashen Yamma, da alama da an riga an samar da rigakafin.
Kaseya ya ce:
“Zan iya gaya muku cewa, da a ce wannan cuta ta bulla a ƙasashen Yamma, da tuni an samar da rigakafi.
"Me ya sa har yanzu ba a samar da wannan rigakafin ba? Saboda wasu daga cikin abokan hulɗarmu sun ɗauki batun a matsayin matsalar Afirka kawai, don haka babu ruwansu.”
Matakan da CDC ta fara dauka
Sai dai shugaban Africa CDC ya ce hukumar na ɗaukar matakai domin magance wannan gibi, ciki har da tallafa wa gwaje-gwajen rigakafin da ake shirin amfani da su.
Ya bayyana cewa wani kamfanin Afirka da ke ƙasar Masar yana gudanar da gwaje-gwajen asibiti kan wani rigakafi da ake fatan zai yi aiki da nau’in Ebola na Bundibugyo.
Kaseya ya kuma ce hukumar na aiki tare da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo da Uganda domin duba yiwuwar gudanar da gwaje-gwaje da kuma amfani da rigakafin Ervebo a ƙarƙashin tsarin jinƙai na musamman.
Sai dai ya bayyana cewa an samar da wannan rigakafi ne domin yaƙi da nau’in Ebola na Zaire.

Source: Getty Images
Afirka na da kwararrun likitoci
Ya jaddada cewa Afirka tana da ƙwararru da kuma ƙarfin da ake buƙata wajen bunƙasa samar da rigakafi, yana mai cewa bai kamata nahiyar ta ci gaba da dogaro kacokan da abokan hulɗa na ƙasashen waje ba a lokutan da annobar cututtuka ta ɓarke.
A halin yanzu, babu wani rigakafin da aka ba da lasisi ko takamaiman maganin da aka amince da shi domin yaƙi da nau’in Ebola na Bundibugyo a nahiyar Afirka.
Martanin Majalisar dinkin duniya
Mun ji cewa Majalisar Ɗinkin Duniya (UN) ta bayyana kwarin gwiwarta kan cewa Najeriya na da karfin shawo kan bullar cutar Ebola ta nau’in Bundibugyo.
Majalisar na cikin damuwa game da gano cutar Ebola ta nau’in Bundibugyo a Najeriya, wadda ta zama ƙasa ta biyar da taNtabbatar da samun bullar cutar a wannan karon.
Asali: Legit.ng
