“Ta Fito Daga Cikin Kudi”: An Gano Hadiza Matar Oba Elegushi Sanye Da Abayar Miliyan N2.9

“Ta Fito Daga Cikin Kudi”: An Gano Hadiza Matar Oba Elegushi Sanye Da Abayar Miliyan N2.9

  • A yanzu haka, Hadiza Adesola Elegushi tana tashe a soshiyal midiya saboda farashin abayar da ta sanya a wani hotonta na baya-bayan nan
  • Wata mai harkar siyar da kasa mazauniyar Dubai ta wallafa hotunan wannan abayar kan farashi N2,980,459
  • Masu amfani da intanet da dama da suka ga wallafar sun je sashin sharhi don yin muhawara kan farashin

A kwanan nan ne aka gano matar Oba Elegushi ta biyu, Hadiza Adeosola Elegushi sanye da wata tsadaddiyar abaya.

Yayin da abayar bai wani banbanta daga sauran abayoyi da aka sani ba, farashin kayan shine babban abun da ya dauka hankali.

Matar Oba Elegushi, Hadiza cikin shiga ta alfarma
“Ta Fito Daga Cikin Kudi”: An Gano Hadiza Matar Oba Elegushi Sanye Da Abayar Miliyan N2.9 Hoto: @olorihadizaelegushi, @hausaroom
Asali: Instagram

Wata mai siyar da kaya mazauniyar Dubai @marsshopdubai, ta wallafa hotunan abaya makamantan wannan kuma a jikin rubutun ta bayyana farashin a kan N2,980,459.

Kalli wallafar a kasa:

Kara karanta wannan

Kudi Masu Gidan Rana: Matashi Ya Kashe Zunzurutun Kudi Fiye Da Miliyan N37 Kan Motar Benz G53, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Shafin Hausaroom ya wallafa hoton Hadiza sanye da abayar kuma mutane sun tofa albarkacin bakunansu kan tsadaddiyar abayar.

Ga ainahin wallafar da Hausaroom ya yi a Instagram:

Jama'a sun yi martani

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanonin jama'a a kasa:

ammnur_kayanmata ta yi martani:

"Allah kayi mana arxiki dawwamamme mai rai."

safiyyahbabashe ta ce:

"Akwai wacca ta fita tsada ma amma duk wanda ta ban taakanina dashi Allah ya kyauta ba godiya dan ya cuceni mil 3 haba inaaaa ba wnn zancen bansan ba dai wanne irin kudi zanyi in sa abayar 3mil duk abayomin duniyar nan yan 12 25."

flats_by_m.a.s ta ce:

"Ni se zooming abayar nake Wlh na kasa gano dalilin da aka saida ta miliyan uku."

mtd_kollection ta yi martani:

"Dana ce muku idan kunji ana ba za’a siya abu ba rashin kudi ne kunyi tunanin wasa nake koh Alaji idan kudin suna nan toh ba’a sanin an kashe su ma Rabbi kawo kudi masu albarka muma sharholiyar nan adan yi damu ."

Kara karanta wannan

Alkali Ya Koka Kan Yawaitar Mace-Mace Aure a Al'ummar Musulmi

mss_jidds ta ce:

"Gaskiya gani nake duk kudin da nayi anya kuwa zan iya saka rigar 3 million kuwa ."

exclusive_veils ta ce:

"@bilkisuayoubd yadda adamu ke zubawa abayas dina wuta ya damki wanan ya nana mata iron a baya i fit craze for this house."

A wani labari na daban, mun ji cewa jama'a da dama sun tausayawa jarumar Kannywood, Rakiya Moussa bayan cin karo da labarin zazzafar soyayyar da take yi wa wani mawaki wanda shi kuma ba haka abun yake a bangarensa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel