Yadda Labarin Zazzafar Soyayyar Da Jaruma Rakiya Moussa Ke Yi Wa Wani Mawaki Ya Girgiza Intanet

Yadda Labarin Zazzafar Soyayyar Da Jaruma Rakiya Moussa Ke Yi Wa Wani Mawaki Ya Girgiza Intanet

  • Jama'a sun tofa albarkacin bakunansu kan halin da jarumar Kannywood, Rakiya Moussa ke ciki
  • Jaruma Rakiya ta fada tarkon son wani mawaki amma kuma shi sam baya yin ta lamarin da ya jefa ta cikin hali
  • Ta kai har ta ce ba za ta taba warkewa daga halin da take ciki na son mawakin ba har duniya ta nade

Shahararriyar jarumar Kannywood wacce ta yi suna wajen fitowa a wakokin soyayya, Rakiya Moussa ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan bayyana da ta yi wata hira mai suna 'Gabon Show'.

A makon jiya ne Hadiza Gabon ta saki bidiyon tattaunawarta da jarumar wacce asalinta yar kasar Nijar ce inda ta bayyana irin zazzafar soyayyar da take yi wani mawaki.

Tun bayan bayyanar bidiyon ne kuma sai jama'a suka yi a caaa a kan lamarin inda kafafen soshiyal midiya suka dauki dumi a kan wannan batu.

Kara karanta wannan

“Ku Ji Idan Da Dadi”: Matashiya Ta Tona Sirrin Zuciyarta Ga Wani Gaye, Ya Ce Baya Yi

Jarumar fim, Raiya Moussa
Yadda Labarin Zazzafar Soyayyar Da Jaruma Rakiya Moussa Ke Yi Wa Wani Mawaki Ya Girgiza Intanet Hoto: Haskenews
Asali: UGC

Mutane da dama sun matukar tausayawa jarumar ganin cewa tana irin soyayyar nan da ake yi wa lakabi da 'son maso wani koshin wahala'.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A hirar tasu, jaruma Rakiya ta ce tsananin son da take yi wa mawakin wanda bata furta sunansa ba, ta na ji a ranta za ta iya rayuwa da shi ko da ace bai da kafa, hannu da duk wasu abubuwan more rayuwa.

An jiyo jarumar tana cewa:

"A tunanina, ace baya da kafa, baya da hannu, baya da abinci, baya da aikin yi, baya da wurin zama a titi yake rayuwa ina ji har gobe har jibi har gata zan iya rayuwa da shi."

Har ila yau jarumar ta ce ba za ta taba warkewa daga soyayyar da take yi wa wannan mawaki ba domin a cewarta babban tashin hankalinta shine ace ta yi aure amma tana dauke da tunani da son wani a zuciyarta.

Kara karanta wannan

“Na Ga Ta Kaina”: Uwa Ta Wallafa Bidiyon Yadda Diyarta Ta Hada Mata Waje, Ta Shige Durowa Ta Yi Zamanta

Ga wani bangare na tattaunawar nasu a kasa:

Jama'a sun yi martani

mufeeda_rasheed1 ta yi martani:

"Kamar a film dama dagaske haka soyayyah take ."

hauwa_yarfulanin_gombe ta ce:

"Nan kusa najima banji abinda ya motsa min rai kaman lamarin yarinyar nan ba wai meyasa duk wanda yake soyayya tsantsa tacika masa kafa,Allah yashiga lamarin ki idan mijinki ne ba makawa inkuwa ba shibane ya kawomiki na kwarai."

safiyyahbabashe ta yi martani:

"Kowa yayi dariya akan abunda mutum yayi kan soyayy ne San menene SO ba wlh Amma ni chilled zobo kan duguza komai a raina ."

neelah_elegance ta ce:

"Har ta ban tausayi."

ammnur_kayanmata ta ce:

"Allah sarki shi so haka yake, baya shawara kuma baya taba tsayawa ya lissafi yaga me zuciya zata shiga, haka zai ta maka radadi."

Matashiya ta mika kokon barar soyayyarta gaban wani saurayi, ya ki amsar tayinta

A wani labarin kuma, mun ji cewa wata matashiyar budurwa ta shiga garari bayan ta fallasa sirrin zuciyarta ga wani saurayi da take matukar so amma ya ki amsar tayinta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel