Kamar Almara: Bidiyon Sauyawar Wani Mutumi Da Ya Yadu Ya Girgiza Intanet
- Wani mutumi ya haddasa cece-kuce a TikTok saboda wani bidiyo da ya wallafa na sauyawarsa a dandalin
- A bidiyon, mutumin ya nunawa mutane yadda kamanninsa yake shekaru biyar da suka gabata da kuma yadda yake a yanzu
- Jim kadan bayan ya wallafa bidiyon mai tsawon sakanni 26, sai mutane suka fara magana, wasu ma na shakku a kan ko da gaske shi din ne
Wani mutumi da ya wallafa bidiyon sauyawarsa a TikTok ya yi fice kuma ya haddasa cece-kuce a dandalin.
Bayan ganin bidiyon wanda @trickyfreshy ya wallafa, wasu masu amfani da TikTok sun gaza yarda da mutumin duba ga yadda ya sauya ya yi haske a sabbin hotunansa idan aka kwatanta da tsoffin.

Asali: TikTok
Shakka babu, manufar mutumin shine nuna yadda jikinsa ya sauya cikin shekaru biyar da suka gabata.
Bidiyon sauyawar wani mutum ya yadu a TikTok
Sai dai kuma ya sauya sosai ta yadda mabiyansa da dama a TikTok suka garzaya sashin sharhi don tambayarsa yadda aka yi ya cimma wannan sabon kamanni nasa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A tsohon hoton, mutumin na dauke da fuska irin na kauraye da yanayin jikinsa da ya yi kama da tsoho, sai dai kuma, ya sauya a sabbin hotunan.
Yanzu ya koma matashi shar da shi ga fatar jikinsa tana sheki wanda gaba daya ya banbanta da yanayinsa na shekaru biyar da suka gabata.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani
@jemi maator ta ce:
"Wanene kuma yake tunanin karya ne."
@celdakayembe ya ce:
"Yaya kake amafani da karya ba tare da yin kasa a gwiwa ba."
@tonyalain ta yi martani:
"Da gaske?"
@nehi ya ce:
"Wannan dan karamin wasan, ka je ka kara da asiri."
@user5693376122293 ya ce:
"Wato kudin ya rage bakin da shekarun?"
@roseu ta ce:
"Karya ne dan Allah! Dogon baki baya tafiya haka."
@rita_uche ta ce:
"Bana tunanin wannan sauyi ne, almara ne."
@beckyodero ya ce:
"Wani abun al'ajabi ne ya faru da fuskarka?"
@giftjames ya ce:
"Ban gane ba."
Budurwa ta koka saboda rashin mashinshini, tana neman mafita
A wani labari na daban, wata matashiya budurwa ta garzaya intanet domin kokawa a kan rashin samun saurayin da zai furta mata soyayya duk da cewar shekarunta 20 a duniya.
Asali: Legit.ng