"Babu Ma'aikacin Da Ke Bi Na Albashi", Gwamna Ikezie IKpeazu

"Babu Ma'aikacin Da Ke Bi Na Albashi", Gwamna Ikezie IKpeazu

  • Gwamnan jihar Abia, Ikezie Ikpeazu ya bayyana cewa ma'aikatan jihar basu bin sa bashin albashi
  • Gwamna Ikpeazu ya musanta cewa ma'aikatan jihar na bin sa bashin albashi wanda bai biya ba
  • Ya bayyana cewa ma'aikatan da bai biya albashi ba, ba shi bane yake da haƙƙin biyan su albashi ba

Jihar Abia- Gwamna Ikezie Ikpeazu na jihar Abia ya musanta cewa ma'aikatan jihar da ƴan fansho na bin gwamnatin sa bashi. Rahoton The Cable

Da yake magana a ranar Alhamis a wata tattauna da gidan talabijin na Channels Tv, Ikpeazu yace ana biyan albashin ma'aikatan jihar na haƙiƙa akan lokaci.

Ikezie
"Babu Ma'aikacin Da Ke Bi Na Albashi", Gwamna Ikezie IKpeazu Hoto: Premium Times
Asali: UGC

A cikin ƴan kwanakin nan dai, zaɓaɓɓen gwamnan jihar, Alex Otti, yayi zargin cewa ma'aikata sun biyo Ikpeazu bashiɓ albashin su sannan ya ƙi ya biya ƴan fansho albashin su na tsawon watanni.

Ikpeazu ya bayyana cewa albashin ma'aikata 29,000 cikin 31,000 an biya shi babu bashin ko kwabo, inda ya ƙara da cewa ragowar 2,000 suna yiwa wasu hukumomi aiki ne.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ƙara da cewa tunda hukumomin suna samarwa da jihar kuɗaɗen shiga ga jihar, su za su biya ma'aikatan su albashi ba gwamnatin jihar ba. Rahoton Within Nigeria

“Bana biya albashin su saboda hukumomin samar da kuɗaɗen shiga ne ga gwamnati." Inji shi
“Bana ƙin sauke nauyin da ya rataya a wuya na. Matsalar fansho ta daɗe tun shekara 24 da suka wuce."
“Nayi iya bakin ƙoƙari na. Wannan gwamnatin sau uku tana shiga cikin karyewar tattalin arziƙi. Lokacin da na kama aiki, a cikin watanni uku na gwamnatina na biya albashin wata 11 da ake bi bashi."
"Wani kawai ya fito ya buɗe baki yace ba a biyan albashi, wannan tsantsagwaron ƙarya ce." Babu wani ma'aikaci na haƙiƙa da yake bi na bashin albashi."

Gwamnan PDP Ya Kori Dukkan Hadimansa Bayan Shan Kaye A Zabe

A wani labarin na daban kuma, gwamnan jihar Abia, ya kori dukkanin hadiman sa daga aiki.

Hakan na zuwa ne bayan ya sha kashi a takarar sanata da yayi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel