Kungiyar Kwadago Ta Janye Yajin Aiki, Ta Ba CBN Wani Sabon Wa'adi

Kungiyar Kwadago Ta Janye Yajin Aiki, Ta Ba CBN Wani Sabon Wa'adi

  • Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) ta dakatar da yajin aikin da ta shirya kan ƙarancin kuɗi
  • Ƙungiyar tace zata jinkirta na tsawon sati biyu domin lura da yadda bankuna za su bi umurnin CBN kan sakarwa mutane kuɗaɗe
  • Ƙungiyar tana da shakku kan cigaba da bin umurnin hakan ya sanya za ta sanya ido har na sati biyu

Abuja- Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) da ƙungiyar Trade Union Congress (TUC) sun dakatar da yajin aikin da suka shirya gudanarwa ranar Laraba kan ƙarancin kuɗi. Rahoton Punch

Ƙungiyoyin biyu sun bayyana cewa za su sanya ido kan wadatuwar kuɗin a bankuna na tsawon sati biyu ƙafin yanke hukunci kan mataki na gaba da za su ɗauka.

Kwadago
Kungiyar Kwadago Ta Janye Yajin Aiki, Ta Ba CBN Wani Sabon Wa'adi Hoto: Leadership
Asali: UGC

Shugabannin ƙungiyon biyu, Joe Ajaero na NLC, da Festus Osifo na TUC, sune suka bayyana hakan a wani taron ganawa da manema labarai a ranar Talata a birnin tarayya Abuja, bayan sun kammala taron su.

Kara karanta wannan

Innalillahi: An Zubar Da Hawaye Yayin Da 'Yan Bindiga Suka Raba Uwa Da 'Ya, Suka Halaka Wata Jaririya a Jihar Arewa

Ajaero yace bayan sun samu bayanai daga shugabannin ƙungiyar na jihohi, sun yanke shawarar jingine umurnin da suka ba ma'aikata na su yi zaman su a gidan makon da ya wuce. Rahoton Leadership

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ajaero ya bayyana cewa:

“Eh, akwai cigaba kan bin umurnin CBN amma NLC bayan taron shugabannin mu, mun sanya shakku kan lokacin da za su kwashe suna bin umurnin."
“Zamu sanya ido kan birnin umurnin zuwa nan da sati biyu domin gane cewa ko zai iya ɗorewa, saboda sun yi gaggawar turowa bankuna kuɗi sannan wasun su har sun fara komawa gidan jiya babu kuɗin."
“Ba dabara bace mu janye yajin aikin cikin gaggawa. A yayin da muka fasa abinda muka shirya, muna so mu ɗan saurara mu gani nan da sati biyu domin ganin yadda lamuran za su kaya."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Tarayya Tayi Magana Kan Zanga-Zangar NLC Kan Karancin Kudi, Ta Bayyana Matakin Da Ta Dauka

"Sun mayar da fannin banki baya. Ƴan Najeriya sun sha matuƙar wahala sosai. Har waɗanda suka samu ciro hey have N10,000 tsoron kashewa suke yi saboda kada ƙarancin ya dawo.
“Ƙungiyoyin NLC da TUC mun yanke shawarar mu tsagaita Laraba ta wuce ba tare da kawo wani cikas ba amma zamu sanya ido nan da sati biyu."

Mun Dakile Shirin NLC", Chris Ngige

Tun da farko rahoto ya zo kan cewa ministan ƙwadago da samar da aikin yi, Chris Ngige, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta dakatar da zanga-zangar da NLC ta shirya gudanarwa kan ƙarancin kuɗi.

Chris Ngige ya bayar da tabbacin shawo kan matsalar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel