“Miliyan N4.8 Nake Biya Kudin Haya Duk Shekara”: Budurwa Ta Baje Kolin Gidanta a Bidiyo

“Miliyan N4.8 Nake Biya Kudin Haya Duk Shekara”: Budurwa Ta Baje Kolin Gidanta a Bidiyo

  • Wata matashiya yar Najeriya wacce ke zama a yankin Lekki na jihar Lagas ta haddasa cece-kuce bayan ta ce tana biyan N4m kudin haya
  • Matashiyar wacce ke da son gayu tana da kwabobi iri-iri a gidanta wanda ke dauke da kayan ado kamar su tsadaddun gashi yan kanti da takalma
  • Mutane da dama da suka kalli bidiyonta sun yi mamakin dalilin da yasa take biyan makudan kudade a gidan haya maimakon gina nata

Lagos - Wani matashi dan Najeriya @walesmorqan, wanda ke yawon tambayan mutane kudin da suke biya na hayar gida a jihar Lagas, ya wallafa bidiyon gidan wata budurwa a Lekki.

A cikin bidiyon, matashiyar ta bayyana cewa naira miliyan 4.8 take biya a matsayin kudin hanayar gida mai dakuna hudu duk shekara. A cewarta, abun da zai fi burge mutum game da gidan shine shirun da ke tattare da zama a wajen.

Kara karanta wannan

Masu Garkuwa Sun Sace Yar Shekara 5 Da Matasa Biyu a Jihar Kwara

Budurwa a cikin hadadden gida
“Miliyan N4.8 Nake Biya Kudin Haya Duk Shekara”: Budurwa Ta Baje Kolin Gidanta a Bidiyo Hoto: @walesmorgan
Asali: TikTok

Attajirar budurwa na biyan N4.8m kudin haya duk shekara

Da aka tambayeta wani irin aiki take yi, matashiyar da ke rayuwa cikin tsadadden gidan ta ce ita din dilalliyar filaye da abun da ya shafi gine-gine ce.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yayin zagawa gidan, matashiyar ta nuna falonta dauke da hadaddun kujeru.

Dakinta yana dauke da wani kwaba da ke kunshe da kayan adonta. Akwai kuma wasu kwabobi dauke da tsadaddun gashi yan kanti, takalma da jakunjunan hannu.

Mutane da dama sun ce lallai ita din attajira ce.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Adebayo tosin ta ce:

"Jinjina ga mutane masu arziki da basa nuna kansu jinjina gare ta."

JERRYBILLIONS ya ce:

"Zan gwammaci gina hadadden gida da ace ina biyan N4.850 duk shekara."

Charity Ogoloma ya ce:

"Yedu tana da matukar kyau tambayeta ko tana bukatar mai aiki."

Kara karanta wannan

“Zan Fasa Auren”: Kyakkyawa Amarya Ta Ajiye Kunya Ta Tika Rawa Iya Son Ranta a Wajen Bikinta, Bidiyon Ya Yadu

piotrbisovetskyi ta ce:

"Kudi na da kyau faaaaaa ina nan enugu ina biyan N300k kudi haya sannan ina ji ni din babbar yarinya ce bani da wayo."

AppleofGodseye05 ta ce:

"Wannan zai iya siyan fili a gari mai kyau sannan na fara gini a kai."

Shekarun matata 21 ba 11 ba, Magidanci ya yi karin haske

A wani labari na daban, wani mutumin arewa da aka zarga da auren karamar yarinya da bata balaga ba ya yi karin haske, ya ce shekarunta 21 ba 11 da wasu ke ta yayatawa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel