Yaro Ya Tsaida Motoci Dake Zargadila Saboda Ya Tada Sallah Akan Titi a Turai, Vidiyon Ya Tada Hazo

Yaro Ya Tsaida Motoci Dake Zargadila Saboda Ya Tada Sallah Akan Titi a Turai, Vidiyon Ya Tada Hazo

  • A wani salon kanku akeji, yaron yasa tsayawa cak saboda mamaki daya bawa mutane dake wucewa na sallah akan titi
  • Baiji maganar da jami’an tsaro ke masa ba akan yabar titi, maimakon haka yaci gaba da sallar sa cike da maida hankali
  • Abin da yaron yayi yasa mutane mamaki, inda wasu suka dauko waya suna yi masa vidiyon da aka daura a yanar gizo gizo har ya kawo kace nace

Wani yaro musulmi ya tada kura a kan hanya, yayin daya shimfida dadduma ya dinga yin sallah abin sa ba tare daya girgiza ko yin gizau ba abinsa.

A wani gajeren bidiyo da aka wallafa a kafar sadarwa ta Tiktok, an hango yaron yana sunkuyawa tare da mikewa, hadi da yin ruku’u da sujjada kamar dai yadda duk wani musulmi yake yi yayin da yake gabatar da sallar sa.

Kara karanta wannan

Ba dani ba: Jama'a sun kadu bayan ganin mutumin da ya reni zakanya tsawon shekaru 11

Tuni dai wannan vidiyon da aka wallafa yaja hankalin masu kallo wanda tuni aka kalle shi kimanin adadi miliyan 6.

Prayer
Yaro Ya Tsaida Motoci Dake Zargadila Saboda Ya Tada Sallah Akan Titin Turai, Vidiyon Ya Tada Hazo Hoto: Legit.ng
Asali: TikTok

Duk da wannan rashin tsoro da yaron ya nuna hade da jarumta, sai da wani jami’in tsaro yaso ya kawar dashi daga kan titi amma hakan ta gagara.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Koda jami’in tsaron yaga haka, sai ya tsaya kusa dashi, ya ci gaba da bashi kariya, tare da bawa ababen hawa hannu a kokarin da suke na wucewa.

Masu wucewa haka suka dinga rabewa suna wucewa, yayin da suka cika da mamakin kallon yaron daya maida hankali cikin natsuwa yana bautawa ubangiji madaukakin sarki.

Yadda mutane suka bayyana ra’ayin su bayan sun kalla:

@Zhaffi4 Yace:

"Ina matukar farin ciki da fararen mutane. Sun san kansu”.

@Austine Abah cewa yayi:

"Hakan ba daidai bane, don Allah ku koya masa yayi abinda ya dace domin maida duniyar wuri mai cike da zaman lafiya”.

Kara karanta wannan

“Ban Gane Ba”: Matashi Ya Sauya Daga Kaura Zuwa Hadadden Gaye, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

@eshunkwabena sai yace:

"Hakan ba daidai bane gaskiya. Ubangiji bazai amshi lamarin bautar nan ba, aikin riya ne ke sawa koda yaushe mutane ke irin wannan bautar. Muyi amfani da kwakwalwar mu ta mutane muyi bauta”.

@Asimike yace:

"Nan gaba yayi ta a tsakiyar babban hanya inya isa, da an kalle ka yadda ya dace”.

@BLESSEDMOMO20 ya kara da cewa:

"Ban san waye ya raini wannan yaron kamar dan Afurka ba”.

@Quamjan ya fusata yace:

"Wannan daukewar hankali ne! Akan me zaa yi ibada akan titi tsakiya? Akan me?

Wani Yaro da Yakewa Mata Addu’a Akan Titi

Wani yaro ya dukufa wajen yiwa mata masu wucewa addu’a akan hanya kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Yaron da yake adduar idon sa a rufe, yana addu’a ne kamar wani wanda yake da wata karama ta hanyar amfani da kalamai daga injila cike da kwarewa.

Matan dake bayan mai daukan vidiyon, akan jiyo su suna ta faman cewa “Amen” ga addu’ar yaron yayin da wasu yara ke kallo daga nesa. Yaron yakan yiwa diyar matan da suke wucewa addua akan allah ya albarkace su.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel