“Rantsar da Tinubu Ya saɓawa Kundin Tsarin Mulki” Inji Baba Ahmed

“Rantsar da Tinubu Ya saɓawa Kundin Tsarin Mulki” Inji Baba Ahmed

  • INEC ta ayyana ɗan takarar jam'iyyar APC na shugaban ƙasa a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban kasa
  • Jam'iyyun adawa sunyi turjiya da amsar sakamakon da hannun daman su, inda kowanne yake iƙirarin shi yayi nasara
  • Baya ga shigar da ƙara da sukayi a kotu, jam'iyyar LP ta hannun mataimakin shugaban ƙasa da yayi mata takara, yace kada Buhari da Alƙalin Kotun koli su kuskura su rantsar da Tinubu

Abuja - Tun bayan ayyana Tinubu a matsayin shugaban ƙasa mai jiran gado, yake ci gaba da samun suka da kira akan duba yadda zaɓen ya kasance daga jam'iyyu daban daban.

Daga ciki akwai korafin jam'iyyar PDP, babbar jam'iyyar adawa ta Atiku Abubakar da kuma jam'iyyar LP ta Peter Obi.

Wannan dalili yasa mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar LP, Datti Baba-Ahmed yayi babban suka akan sahihancin rantsuwar da ake ƙoƙarin yiwa Bola Ahmed Tinubu a 29 ga Mayu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gawuna Yayi Magana Kan Sakamakon Zaben Gwamnan Kano, Ya Bayyana Abinda Yakamata INEC Tayi

Baba-Ahmed 3
Rantsar da Tinubu Ya saɓawa Kundin Tsarin Mulki Inji Baba Ahmed Sanda Ya Roƙi Buhari da Shugaban Kotun Ƙoli
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Baba Ahmed yayi wannan batun ne a wani shiri mai suna "Television's Politics Today" da ake na kai tsaye wanda ya samu halarta a ranar laraba.

Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasan yace, APC bata cika ƙa'idar sashi na 134 (2)(a) da kuma (b) na kundin tsarin mulkin Najeriya wanda ke magana akan yadda za'a zaɓi shugaban ƙasa.

A cewar sashin, duk wani halastaccen shugaban ƙasa shine wanda "Yake da mafi yawa na adadin kuri'un da aka kaɗa a zaɓe" kuma "Shine wanda bai da ƙasa da kashi ɗaya cikin huɗu na akalla kashi biyu bisa ukun ƙuri'un da aka kaɗa na dukkan jihohin Najeriya da babban birnin tarayya, Abuja ba".

Saboda haka ne, yayi kira ga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da Shugaban Kotun Ƙoli, Justice Olukayode Ariwoola suyi biyayya ga wannan sashe, inda yace rantsar da Tinubu tamkar fatali da wancan sashen ne.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Mummunar Gobara Ta Sake Tashi a Wata Babbar Kasuwa, Miliyoyin Naira Sun Salwanta

A cewar Baba Ahmed:

"Mai girma shugaban ƙasa, kada ka rantsar dashi. Alƙalin kotun ƙoli, da martabar ofishin ka, kaima kada ka shiga cikin wannan lamari dake saɓawa kundin tsarin mulkin Najeriya". inji sa.

Gidan talabijin na Channels TV ya ruwaito Baba-Ahmed yana cewa, rantsar da ɗan takarar da bai cika ƙa'idar zaɓe sahihi ba, tamkar ruguje tare da lalata tsarin demokradiyya ne.

A cewar sa:

"Wannan shine fassara ta da sashin, kuma tabbas bana tantama, haka shine daidai".

Baba Ahmed ya ƙara da cewa:

"Babu yadda za'ai ka rantsar da mutanen da basu cika ƙaidar kundin tsarin mulki ba, ai bazata saɓu ba, wai bindiga a ruwa".

Ya nisa ya ƙara da cewa:

"Idan har kayi hakan, kayi abinda yake ya saɓawa doka da oda tunda ya sabawa Kundin tsarin mulki".

Dan takarar ya ƙarkare da zargin Shugaban hukumar zaɓe ta ƙasa Mahmood Yakubu da saka rayuwar ƴan Najeriya a hatsari ta hanyar damƙawa Tinubu shaidar cin zaɓe, abinda yace shi bazai iya hakan ba idan da shine.

Kara karanta wannan

2023: APC Ta Yi Babban Abun Kunya, Jam'iyar PDP Ta Kwace Kujerun Yan Majalisu 25 Cikin 26 a Jiha 1

“Ma'aikatan Najeriya Ku Fita Zanga-Zanga Daga Litinin Saboda Ƙarancin Kuɗi” inji Kungiyar Kwadago Alhamis

Tun bayan da zaɓe yazo ya tafi har yanzu ba'a fita daga cikin yanayin ƙarancin kuɗaɗe dake yawo a hannun jama'a ba.

Wanda hakan ne yasa Ƙungiyoyin fafutukar kare yancin ma'aikata suka shiga gwagwarmayar tunda an harzuka su da lamarin da yake tafiyar wahainiya.

Legit.ng ta ruwaito yadda Ƙungiyar Ƙwadago ta ƙasa ta umarci duk wani mamban ta daya shirya zanga-zanga daga sati me zuwa a ofisoshin CBN na kowacce jiha.

Asali: Legit.ng

Online view pixel