25 Sun Mutu, 10 Sunji Munanan Raunuka a Wani Mummunan Hatsarin Mota a Bauchi

25 Sun Mutu, 10 Sunji Munanan Raunuka a Wani Mummunan Hatsarin Mota a Bauchi

  • Haɗarin ya faru ne akan hanyar Hadeja-Potiskum ta zuwa ƙaramar hukumar Gamawa dake jihar Bauchi
  • Direban motar ya rasa yadda zai sarrafa motar ne, wanda hakan yasa ya aukawa wasu mutane 11 dake hutawa a ƙarƙashin wata bishiya
  • Hukumar FRSC ta Bauchi tace hatsarin ya faru ne saboda taƙe motar da akayi da kaya masu yawa, da gudun wuce sa'a, da yasa tayar motar ta fashe

Bauchi - Idan ajali yayi kira ko babu ciwo dole aje. Mutuwa kenan, mai raba bawa da rai, bawai don baya so ba.

Ita mutuwa ko babu ciwo idan lokaci yayi, tafiya akeyi bagatatan.

Mutuwar ita tazo wa wasu mutane kimanin 25 dake tsaka da tafiya akan hanyar su ta Hadeja-Potiskum, dake cikin ƙaramar hukumar Gamawan Jihar Bauchi.

Bauchi Crash
25 Sun Mutu, 10 Sunji Munanan Raunuka a Wani Mummunan Hatsarin Mota a Bauchi Hoto: The Punch Asali: UGC
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: DSS Ta Damƙe Ɗan Majalisa Kan Hannu a Laifin da Ya Shafi Karancin Naira

Duk dai a cikin mummunan hatsarin, wasu daga cikin mahayan kimanin guda 10 sun samu munanan raunuka a cikin motar dake tsaka da zabga gudu.

Lamarin maras daɗin ji da gani ya faru ne ranar Alhamis, da misalin ƙarfe 4:30 na yamma.

Kwamandan rundunar kare haɗurra ta ƙasa sashin jihar Bauchi, Yusuf Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin ga Jaridar Punch a safiyar yau juma'a.

Jami'in yace, a cikin mutanen 35 akwai maza 19, mata 11, yara maza guda 2 da kuma yara mata guda uku.

Da jami'in yake zayyana yadda haɗarin ya faru, yace, direban motan da tayi haɗari, ya rasa yadda zai sarrafa motar ne, wanda hakan yasa ya aukawa wasu mutane 11 dake hutawa a ƙarƙashin wata bishiya dake kusa da wajen wankin mota.

Ga yadda Abdullahi, ya zayyana lamarin:

"Kwarai kuwa, an samu mummunan hatsarin mota a Udubo, akan hanyar Hadeja-Potiskum ta zuwa ƙaramar hukumar Gamawa dake jihar Bauchi. Hatsarin ya faru jiya Alhamis, watau 23rd ga watan Maris na 2023." inji shi.

Kara karanta wannan

2023: Jerin Jihohin da Ba'a Kammala Zaben Gwamna Ba da Waɗanda INEC Ta Dakatar da Tattara Sakamako

"Hatsarin ya haɗa da wata motar haya samfurin Toyota Hummer Bus mai lamba 'JMA 59XA'.",
"Hatsarin ya faru ne saboda taƙe motar da akayi da kaya masu yawa, gudun wuce sa'a, da yasa tayar motar ta fashe har motar ta ƙasa sarrafuwa." Inji shi.

Jami'in ya tabbatar da cewa, sun isa wajen ne bayan samun sanarwar faruwar lamarin, inda basui wata wata ba, suka tura jami'an su na ujula domin basu tallafin gaggawa.

Koda suka isa asibiti da masu hatsarin ne aka tabbatar da cewar, mutane 25 sun sheka barzahu yayin da 10 ke ci gaba da amsar magani sakamakon mummunan ciwo da suka ji a jikkunan su.

Gawarwakin wanda suka mutu an ajiye su a dakin ajiye gawa na FMC, Azare.

Daga ƙarshe, bayan jimamin lamarin, jami'in yayi kira ga matuƙa dasu kula sosai wajen bin dokokin tuki, domin rage haɗurra dake sawa a rasa rai da kuma sawa aji ciwo.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An Bindige Tsohon Kansila A Kano Har Lahira Kan Sace Akwatin Zabe

Yan Jagaliya Sun Cinnawa Motar Wani Zaɓaɓɓen Dan Majalisa Wuta

Yan jagaliyar siyasa na cigaba da cin karen su babu babbaka, yayin da suka ƙaddamar wa da zaɓaɓɓen ɗan majalisa Aondona Dajoh mai wakiltar Gbemacha a yau juma'a.

Yan jagaliyar sun cinnawa motar Dajoh wuta ne da misalin ƙarfe 10 na dare, amma rahoto ya nuna bai samu koda ƙwarzane ba, domin zakara ya bashi sa'a.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewar, Catherine Anene dake zama kakakin yan sandan jihar Benuwai ta tabbatar da harin da aka kai wa zababben ɗan majalisar.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel