DSS Ta Kama Zababben Dan Majalisar Dokokin Ogun Kan Zargi 1

DSS Ta Kama Zababben Dan Majalisar Dokokin Ogun Kan Zargi 1

  • Jami'an tsaron DSS sun kama ɗan majalisar jiha mai jiran gado a jihar Ogun, Damilare Bello, kan zargin hannu a shirya zanga-zanga
  • Wata majiya a DSS ta ce jami'ai suna damke Belle ne bayan kin amsa gayyatar da aka aika masa lokuta da dama
  • A watan Fabrairu fusatattun matasa suna kona bankuna aƙalla 10 a garin Sagamu kuma ana zargin yana da hannu

Ogun - Dakarun hukumar tsaro (DSS) sun cafke zababben ɗan majalisar jiha mai wakiltar Sagamu 1, Damilare Bello.

Ana zargin Bello da kitsa ɗanyen aikin da aka aikata a Sagamu wanda ya yi sanadin lalata bankuna da yawa lokacin zanga-zangar ƙarancin naira.

Wakilin jaridar Punch ya tattaro cewa wanda ake zargin ya yi fatali da takardar gayyatar da DSS ta aiko masa lokaci da dama, ya ƙi zuwa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnan APC Ya Sha Da Ƙyar, Ya Lashe Zaben Gwamna a Jiharsa

Jami'an DSS.
DSS Ta Kama Zababben Dan Majalisar Dokokin Ogun Kan Zargi 1 Hoto: punchng

Haka nan an ce tun bayan faruwar wannan tashin-tashina, Bello, wanda ya fi shahara da Dre ya gudu aka daina ganinsa har sai lokacin zabensu ranar Asabar da ta gabata.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Meyasa DSS suka kama Bello?

Wata majiya a cikin jami'an DSS ya ce sun kama Bello ne kan zanga-zangar da aka gudanar ranar 20 ga watan Fabrairu a garin Sagamu, ƙaramar hukumar Sagamu a jihar Ogun.

Yayin wannan zanga-zanga, wasu daga cikin matasan kabilar Irate suka yi kaca-kaca da bankuna 10 da wasu gine-gine mallakin gwamnati.

Majiyar ta ce"

"Ranar 21 ga watan Maris, 2023 da misalin ƙarfe 2:30 na rana, hukumar DSS ta kama Oluwadamilare Bello bisa zarginsa da haɗa baki wajen aikata zagon ƙasa ga tattalin arziki."
"An fara gudanar da bincike kuma da yawuwar a gurfanar da wanda ake zargin gaban kuliya bisa tuhumar cinna wuta da kuma gurɓata zaman lafiya da sauransu."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An Bindige Tsohon Kansila A Kano Har Lahira Kan Sace Akwatin Zabe

"Wannan matakin na kama Bello ba shi da alaka da siyasa kamar yadda wasu su ke yaɗawa."

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa tun bayan kama ɗan siyasan, PDP take tura wakilai ofishin DSS cikin har da ɗan takarar gwamna, Oladipupo Adebutu.

Gwamna Umahi Ya Baiwa Atiku Abubakar da Peter Obi Shawara

A wani gefen kuma, Gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi ya nemo wa Atiku da Peter Obi mafita bayan sun sha kaye a hannun Tinubu

Umahi ya roki manyan yan takarar biyu sun janye ƙarar da suka shigar gaban Kotu su fawwala wa Allah komai kuma su hada hannu a matsar da ƙasar nan gaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel