Farashin Kayan Abinci Ya Yi Tashin Gwauron Zabi Yayin da Yan Kasuwa Suke Karbar Tsoffin Kudi a Taraba

Farashin Kayan Abinci Ya Yi Tashin Gwauron Zabi Yayin da Yan Kasuwa Suke Karbar Tsoffin Kudi a Taraba

  • Bayan dawo da amfani da tsoffin kudi a kasar, kayan abinci da dabbobi sun yi tashin gwauron zabi a wasu kasuwanni
  • A kasuwar mako da ke ci a jihar Taraba, yan kasuwa sun karbi tsoffin kudi amma farashin kaya sun sha banban da na makon jiya
  • Buhun masara da aka siyar N14,000 a makon jiya, ya koma N17,000 a jiya Talata, 14 ga watan Maris

Taraba - Farashin kayan hatsi da dabbobi ya tashi sama a ranar Talata, 14 ga watan Maris a kasuwar mako na Iware da ke jihar Taraba yayin da tsoffin kudade suka bazu.

Daily Trust ta rahoto cewa yan kasuwa a kasuwar da ke ci duk ranar Talata sun karbi tsoffin kudade.

An tattaro cewa hakan ya sa an samu kari a farashin kayan hatsi da dabbobi a kasuwar.

Kara karanta wannan

Ganduje Ya Jajantawa Yan Kasuwar Kano Da Gobara Ya Shafa

Kasuwar kayan hatsi mai ci
Farashin Kayan Abinci SYa Yi Tashin Gwauron Zabi Yayin da Yan Kasuwa Suke Karbar Tsoffin Kudi a Taraba Hoto: Katsina Post
Asali: UGC

A makon jiya, an siyar da kayan hatsi da dabbobi a farashi mai rahuda saboda rikicin tsabar kudi amma lamarin ya sauya a wannan Talatar kasancewar an karbi tsoffin kudi a kasuwar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda farashin kayayyaki yake tsakanin makon jiya da yanzu

An siyar da buhun masara yar 100kg kan N14,000 a makon jiya amma a jiya Talata N17, 000 aka siyar da shi.

Buhun shinkafa shanshara da aka siyar N16,000 a makon jiya ya kasance N18,000 zuwa N20,000 a jiya Talata, rahoton Aminiya.

Bincike ya kuma bayyana cewa babban saniya da aka siyar N270,000 da tsabar kudi a makon jiya yanzu ya koma N320,000.

Wasu yan kasuwa sun bayyana cewa karbar tsoffin kudi da aka yi a kasuwar ya bunkasa harkokin kasuwanci.

Wani dan kasuwa, Sani Faruk, ya bayyanawa jaridar cewa a makonnin Da suka gabata, masu siyan kayayyaki yan kadan ne suka fito kasuwa saboda karancin tsabar kudi, wanda hakan yasa dole aka karya farashin kayayyaki a kasuwar.

Kara karanta wannan

Tattalin Arziki: Yadda Najeriya Tayi Asarar Naira Tiriliyan 20 a Yunkurin Canza Kudi

Gobara ta lakume shaguda da miliyoyin dukiya a kasuwa Singa ta jihar Kano

A wani labari na daban, mun kawo cewa a farkon makon nan ne mummunar gobara ta tashi a shahararriyar kasuwar nan ta Singa wacce ta yi fice wajen siyar da kayan abinci a jihar Kano.

Wannan ibtila'i ya lakume shaguna da dama inda yan kasuwa suka yi asarar miliyoyin dukiya, wasu kuma sun samu damar kwashe dan abun da ya yi saura daga dukiyoyinsu.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel