Tashin Hankali Yayin da Gobara Ta Tashi a Fitacciyar Kasuwar Singa Ta Jihar Kano

Tashin Hankali Yayin da Gobara Ta Tashi a Fitacciyar Kasuwar Singa Ta Jihar Kano

  • Yan kasuwa a kasuwar Singa ta jihar Kano sun gamu da babban ibtila'i a ranar Litinin, 13 ga watan Maris
  • Mummunar gobara ta lakume dukiya a kasuwar da ta yi suna wajen siyar da kayan abinci
  • Hukumar kashe gobara na ta kokarin daidaita wutar wacce ta fara ci tun da tsakar daren ranar Lahadi

Labari da muke samu daga Freedom Radio shine cewa har yanzu ba kai ga kashe gobarar kasuwar Singa ta jihar Kano.

Mummunar gobara ta tashi a shahararriyar kasuwar nan ta siyar da kayan abinci ta Singa da ke jihar Kano a tsakar daren Lahadi wayewar garin Litinin, 13 ga watan Maris.

Wasu da abun ya faru a kan idanunsu sun bayyana cewa gobarar ta fara ci ne a tsakar dare kuma an gagara shawo kanta har zuwa wayewar garin Litinin, rahoton Aminiya.

Kara karanta wannan

Sauya Naira: Manyan Arewa Sun Fada Wa Shugaba Buhari Abinda Zai Faru Idan Ya Ki Bin Umarnin Kotun Koli

Kasuwar Singa da ke jihar Kano yayin da gobara ta tashi
Tashin Hankali Yayin da Gobara Ta Tashi a Fitacciyar Kasuwar Singer Ta Jihar Kano Hoto: Freedom Radio Nigeria
Asali: Facebook

Jami'an hukumar kwana-kwana da ke kashe gobara suna nan suna ta kokarin shawo kan wutar wacce ke ci gaba da ci a bangarorin kasuwar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yanzu haka da yawa a cikin yan kasuwar na ta kokarin kwashe iya abun da ya sawwaka daga dukiyoyinsu da suka yi saura a kasuwar ta Singa.

A halin da ake ciki, an tattaro cewa gobarar ta lakume shaguna da rumbunan ajiya da dama, wanda hakan ya sa yan kasuwar asarar miliyoyin Naira.

Ga karin hotuna a kasa:

Gobara ta tashi a kasuwar Rimi

Hakan na zuwa ne yan kwanaki bayan wani lamari makamancin wannan ya faru a kasuwar Rimi da ke jihar ta Kano.

Legit.ng ta tattaro cewa gobarar da ta tashi a kasuwar Rimin ta lakume shaguna guda 21 a nan take.

Kara karanta wannan

2023: CAN Ta Fada Wa Kiristoci Yan Takarar Da Za Su Kada Wa Kuri'a A Zaben Gwamnoni Da Majalisar Jiha

A yan baya-bayan nan, ana yawan samun tashe-tashen gobara a kasuwanni daga sassa daban-daban na kasar lamarin da kan jefa yan kasuwa cikin halin wayyo Allah. Wasu ma daga nan ne suke samun karayar arziki

Mummunar gobara ta tashi a kasuwar Borno

A wani labarin kuma, mun ji cewa a makonni biyu da suka gabata ne wata gobara ta lakume miliyoyin naira a shahararriyar kasuwar 'Monday Market' da ke jihar Borno.

Gobarar ta tashi ne da tsakar dare inda ta dungi ci har wayewar gari kuma ko sama ko kasa aka rasa musababbin tashinta inda yan kwana-kwana suka dungi kokarin ganin sun shawo kanta.

Da yake martani Daraktan Hukumar kwana-kwana ta jihar Borno, Umaru Kirawa yajami'ansu a matakin jihar da na tarayya daga bangarori daban-daban sun hada hannu don dakile annobar.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel