Yan Sanda Sun Ceto Mutane 14 da Aka Yi Garkuwa da Su a Zamfara

Yan Sanda Sun Ceto Mutane 14 da Aka Yi Garkuwa da Su a Zamfara

  • Dakarun 'yan sanda sun samu nasarar tarwatsa sansanin yan fashin daji yayin da suka fita Operation wani daji a Zamfara
  • Mai magan da yawun rundunar yan sandan jihar, Muhammad Shehu, ya ce jami'ai sun ceto mutane 14 a samamen
  • Kwamishinan 'yan sanda ya ce hukumar ba zata yi ƙasa a guiwa ba wajen kare rayuka da dukiyoyin jama'a

Zamfara - Rundunar 'yan sanda ta samu nasarar tarwatsa sansanin yan bindiga kuma ta kubutar da mutane 14 da aka yi garkuwa da su a jihar Zamfara.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan Zamfara, Muhammad Shehu, ne ya faɗi haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Gusau, ya ce mutanen sun kwashe kwanaki 68 a Jeji.

Jami'an yan sanda.
Yan Sanda Sun Ceto Mutane 14 da Aka Yi Garkuwa da Su a Zamfara Hoto: Policeng
Asali: UGC

Premium Times ta rahoto kakakin 'yan sandan na cewa:

Kara karanta wannan

Yanzun Nan: Tsageru Sun Kaiwa Ayarin Ɗan Takarar Gwamna Mummunan Hari a Kaduna, Sun Tafka Ɓarna

"Ranar 10 ga watan Maris, dakarun 'yan sanda da haɗin guiwar 'yan banga suka fita shara a Jejin Munhaye, sun yi nasarar tarwatsa sansanin 'yan fashin daji mallakin kasurgumin ɗan bindiga, Dogo Sule."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Sakamakon wannan samame, jami'an tsaron sun ceto mutane 14 da suka kunshi maza samari 2, mata 7 da kananan yara 5 da ke ƙasa da shekara biyu a duniya."
"Mutanen sun gaya wa 'yan sanda cewa ranar 1 ga watan Janairu, 'yan bindiga suka shiga Anguwan Mangoro da Gidan Maidawa, Gusau LG, suka yi awon gaba da su zuwa sansaninsu."
"Mutanen suna cikin mawuyacin hali kuma tuni aka garzaya da su Asibtin 'yan sanda da ke Gusau domin ba su kulawa daga bisani a haɗa su da iyalansu," inji shi.

Shehu ya ƙara da cewa kwamishinan 'yan sandan Zamfara, Mista Kolo Yusuf, ya taya mutanen da aka ceto murnar shaƙar iskar 'yanci.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin Da Yan Ta'adda Suka Tafi Har Gida Suka Kashe Ɗan Malamin Addini, Sace Matarsa A Kaduna

Haka zalika ya ƙara tabbatarwa da al'umma cewa hukumar 'yan sanda ta shirya tsaf domin ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin 'yan Najeriya, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

An Gano Gawar Mutane 10 Bayan Harin Yan Bindiga a Kaduna

A wani labarin kuma An shiga yanayin tashin hankali bayan yan bindiga sun kai wani mummunan hari a jihar Kaduna

Bayanai sun nuna cewa kawo yanzun an gano gawar mutane 10 a Unguwar Wakil dake karamar hukumar Zangon Kataf, Kaduna.

Gwamnatin ƙaramar hukumar ta sanar da sanya dokar kulla tsawon awanni 24 a garuruwa 4 domin baiwa sojoji damar dawo da zaman lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel